Dalilin da ya sa ban halarci taron jam’iyyar APC ba – Buhari
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa bai halarci taron jiga-jigan jam’iyyar APC ba.
Jam’iyyar APC mai mulki ta tsaida ranakun 2 da 3 ga watan Agusta domin gudanar da taron jiga-jigan jam’iyyar na kasa da na kwamitin zartarwa na kasa (NEC).
KARANTA WANNAN LABARIN:Da dumi-dumi: Mai baiwa APC shawara kan harkokin shari’a ya yi murabus
Taron na kasa ya gudana ne a fadar shugaban kasa a ranar Laraba, yayin da babban taron shugabannin jam’iyyar zai gudana a Transcorp Hilton a yau (Alhamis).
Akan dalilin da ya sa Buhari ya kasa halartar taron, Garba Shehu, mai magana da yawunsa, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce tsohon shugaban ba ya zuwa saboda wasu ayyuka da yake yi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin halartar taron jam’iyyar da kuma kwamitin zartarwa na kasa, NEC, na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, wanda aka gayyace shi.
“Ya mika uzurinsa, wanda ke nuni da cewa ba zai iya zuwa ba saboda alkawuran da aka yi a baya.
“Tsohon shugaban kasar ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana goyon bayansa da jajircewarsa ga jam’iyyar, tare da yi mata fatan haduwa da juna, yayin da shugabannin ke daukar matsaya kan batutuwa masu muhimmanci ga jam’iyyar da kasa baki daya.
Ku tuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kuma nemi afuwar rashin zuwansa a wajen taron.
Osinbajo yace ya jajirce akan ayyuka da dama a wajen kasar.
A ranar 17 ga watan Yuli ne jam’iyyar APC ta sanar da dakatar da taron jiga-jigan jam’iyyar na kasa baki daya.
Abubakar Kyari, mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya yi magana bayan taron gaggawa na kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC).
Taron na NWC wanda ya gudana a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, an kira shi ne bayan murabus din Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa kuma sakataren jam’iyyar na kasa, bi da bi.
Kyari ya ce canjin shugabancin jam’iyyar ne ya sa aka dage taron.
A wani labarin kuma:Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
An nada tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa
An nada Ganduje a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa a ranar Alhamis