Dalilin da ya sa na boye matata da ’ya’yana daga shafukan sada zumunta – Chinedu Ikedieze
Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Chinedu Ikedieze, wanda aka fi sani da Aki, ya bayyana dalilin da ya sa yake boye iyalansa daga shafukan sada zumunta.
Mai shekaru 45 ya ce ba ya bari matarsa da ‘ya’yansa su shiga shafukan sada zumunta saboda yana son su sami ‘yanci.
KARANTA WANNAN LABARIN:Budurwa Ta Nemi Sadakin Naira Miliyan 76, Gidaje 3, Motar Zinare Daga Hannun Wanda Zai Aureta
Ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da fitaccen dan jarida Chude Jideonwo.
Ya ce, “Ina da ‘ya’ya amma na yanke shawarar ajiye su a gefe saboda ni ne shahararren, ba su ba.
“Ina so kawai su sami ‘yanci saboda duk lokacin da kowa ya san su, zai taɓa su. Kuma ba na son hakan.
“Don haka, na boye su har da matata ban da sanarwar aurenmu da na yi, don ta iya zuwa kasuwa, ta yi duk wani abu ba tare da wani tashin hankali ba.”
DAILY POST ta tuna cewa Ikedieze ya auri matarsa Nneoma Nwaijah a shekarar 2011.
Ma’auratan sun sami albarka tare da ‘ya’ya amma dan wasan ya yanke shawarar ɓoye cikakkun bayanai akan su.
A wani labarin kuma:Italiya Ta Nada Sabon Kocin Tawagar Kasar
Kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya bayyana cewa babu wani shiri na tsige mataimakin gwamna Philip Shaibu
Labarin tsige mataimakin gwamnan jita-jita ce kawai, domin gwamna ba shi da irin wannan shiri
Kakakin majalisar ya bayyana hakan ne ya yin da ‘yan majalisar dokokin jihar suka ziyarci Gwamnan