Babban Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta ƙasa(NPA) Muhammed Bello Koko ya bayyana cewa manyan manyan jiragen ruwan da ake amfani da su wurin satar ɗanyen mai ba za iya gano su ba, saboda sun kashe na’urorin da ake amfani da su wurin bin diddigin su wato (AIS). Kamar yadda Channels TV ta ruwiaito.
Koko ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja , inda ya ce an katse na’urorin da ke samar da bayyanan manyan jiragen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: CBN Zai Sauya Tsarin Wasu Takardun Kuɗin Najeriya
Ya bayyana cewa mahukunta basu da isasun kayan aiki na zamni da suke buƙata waɗanda za su basu damar iya gano inda manyan jiragen ruwan suke.
Da yake jawabi akan wata matsalar da ta auku inda wata babbar motar dakon mai da aka kama ɗauke da ɗanyen mai babisa ƙaidaba, Daraktan Hukumar ta NPA Muhammad Bello Koko yace hukumar na shirye-shiryen ƙaddamar da wata sabuwar fasaha mai suna (VTS) wanda zata bata damar bibiya tare da gano dukkanin manyan manyan jiragen ruwan da ke faɗin ƙasar nan.
Daraktan ya bayyana cewa , hukumar ta ɗauki tsawon shekaru goma tana ƙoƙarin mallakar na’urar kuma yanzu ta samu sahalewa daga hukumomin da abun ya shafa, ya ƙara da cewa hukumar na aiki tare da kamfunan man gasa na ƙasa domin ƙarfafa samun damar gano waɗannan jiragen ruwan.
Koko ya bayar da tabbbacin cewa za a sayo na’urorin kafin ƙarshen wa’adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
A ɗan wannan lokacin Batun Satar ɗanyen mai ya mamaye kanun jaridun dake fadin ƙasar nan, Inda aka ambato tsohon Gwamnan Babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi da gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmed Elrufa’i ke buƙatar da a mayar da kamfanin mai na ƙasa (NNPC) mai a mai zaman kansa.
Domin nuna damuwar ta akan wannan mumunar lamarin , a watan Augusta da ya gabata gwamnatin tarayya ta ba wani kamfani da ke karkashin jagorancin tsohon shugaban ‘ masu tayar da ƙayar baya Ekpemepulo wanda aka fi sani da Tompolo kwangilar kula da bututun mai,
Sai dai wannan Lamarin ya janyo suka daga ‘yan Najeriya da dama, ciki har da fitaccen lauyan nan , Femi Falana, wanda ya bayyana lamarin a matsayin babban abin kunya ga hukumomin tsaron dake faɗin Najeriya
To sai dai A cikin watan Agusta, babban Daraktan kamfanin mai na ƙasa NNPC, Mele Kyari, ya bayar da hujja tare da kare matakin bayar da kwangilar sa ido kan bututun mai wanda gwmamnatin tayi , kuma aikin zai laƙume biliyoyin kuɗi ga kamfanin tsaro na Tantita wanda ke karkashin jagorancin Tompolo.
Idan ba a mantaba, bada jimawa ba ne kamfanin Tompolo ya ayyana banƙaɗo wurin da ake satar danyen mai a yankin Niger Delta.
A cewar Tompolo, ya zuwa yanzu an gano haramtattun wuraren mai guda 58 tun bayan da kamfanin ya fara aikin kawo karshen satar mai a hanyoyin ruwa dake jihohin Delta da Bayelsa.
A WANI LABARIN KUMA: Paskistan Ta Aike Da Tawaga Zuwa Ƙasar Kenya
Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya sanar da kafa wani kwamitin bincike da zai je kasar Kenya domin gudanar da bincike.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa za a gudanar da binciken ne kan halin da ake ciki a kisan dan jarida Arshad Sharif, wanda aka harbe shi a birnin Nairobi a daren Lahadi