Wata shugabar mata a jam’iyyar APC a jihar Kwara, Hajiya Hud Shekinat, ta yi kira ga al’ummar jihar da su goyi bayan sake zaben gwamna AbdulRahman AbdulRazaq a karo na biyu, inda ta ce babu wata gwamnati tun da aka kirkiri jihar ta baiwa mata karramawa fiye da na shugaba mai ci.
Da take magana a wani taron manema labarai da addu’o’in da AbdulRahman AbdulRazaq Progressive Platform ya shirya na sake tsayawa takarar Gwamna AbdulRazaq a Ilorin ranar Lahadi, Hud ta ce gwamnan a wa’adinsa na farko ya fi mai da hankali kan harkokin mata a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Burin Peter Obi Shine Ya Maida Tinubu Shugaban Kasa — Keyamo
“AA ya sa mun yi alfahari a matsayinmu na mata a jihar a wa’adin mulkinsa na farko, shi ne ya kawo mu ga fitattun mutane. Ba a takura mu a madafar abinci ba kamar yadda wasu ke cewa don haka ba mu da wani zabi da ya wuce mu goyi bayan zaben sa don a ci gaba da ayyukan alheri.
“Babu wani dan takara da yake da karfinsa da kwarewarsa, don haka muna goyon bayan Gwamna AbdulRazaq saboda abin da yake yi, musamman ga mata,” in ji ta.
Ta kara da cewa mata sun kuma ci gajiyar tallafin karatu, gina hanyoyi, karfafawa da dai sauransu. Mun amfana fiye da yadda muka samu a cikin shekaru 16 da suka gabata.”
Shima da yake nasa jawabin a cikin shirin, wani likita kuma daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Kwara, Alhaji Azeez Adebayo, ya ce gwamnatin gwamna AbdulRazaq Allah ne ya kafa ta a tarihin kafa jihar. Don haka ya yi kira da a sake zabensa a zaben ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023.
Adebayo, shi ne mai kiran AbdulRahman AbdulRazaq Progressive Platform, ya ce, “Gwamnatin Mallam AbdulRahman AbdulRazaq Allah ya yi masa jagoranci, shi ya sa a cikin shekaru hudu da suka gabata nasarorin da ya samu ya zarce abin da gwamnatocin baya suka yi a shekaru 16 da suka gabata.
“Tambarin gwamnatin gwamna AbdulRazaq na gaskiya kuma mai son jama’a ana jin ta a ko’ina a fadin jihar saboda yana tausaya wa talakawa kuma yana da sha’awar ciyar da jihar gaba.
“Don haka duk abin da ‘yan jam’iyyar adawa ke cewa yanzu a yi watsi da su domin babu abin da za su iya bayarwa, makiyan jihar Kwara ne.
“Wadanda ke zaune a Kwara za su san cewa gwamnatocin da suka gabata sun raba kason kasa tun daga lokacin da aka kirkiro ta kuma ba su yi komai ba don ci gaban jihar.”
A nasa jawabin babban ko-odinetan kungiyar AAPP, Alhaji Ayuba Aduragba, ya zayyana manyan nasarorin da Gwamna AbdulRazaq ya samu a cikin shekaru hudu da suka gabata, ya kuma yi kira ga kowa da kowa da a sake zabensa a zaben ranar Asabar mai zuwa.
“Muna kira ga kowa da kowa da su zabi gwamna AbdulRazaq a ranar Asabar domin a ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da kuma kara aiwatar da ayyukan raya kasa domin amfanin al’umma baki daya,” inji shi.
A wani labarin kuma, Dalilin da ya sa ba zan sake tsayawa takarar Shugaban kasa ba – Wike
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takarar shugaban kasa ba.
Wike a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a lokacin yakin neman zaben gwamna, ya ce mulki zai koma Arewa bayan shekaru takwas na Kudu.