Mahaifiyar dan takarar gwamnan a Jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusif, wato Hajiya Mowa Sufi Yakasai ta rasu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Marigayiya Hajiya Mowa ta rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya.
Yanzu-yanzu: Za Ka Iya Yin Rashin Nasara A 2023, Wike Ya Fadawa Aiku
Ta rasu ne tana da shekaru 103 a duniya, kuma ta bar yaya da jikoki da dama.
Daga cikin ya’yan nata akwai sakataren Mulki a Kwalejin Shari’a ta Aminu Kano wato Legal, (AKCILS) Ibrahim Abubakar.
Tuni dai aka yi mata jana’iza (sutura) a babban masallacin juma’a na cikin garin Kano, da aka fi sani da masallacin Sarki.
Tana dai da tarin jikoki baya ga yaya, wanda cikinsu kuma akwai wani babban likita a Asibitin Murtala Muhammad wato Dr Atiku Musa.