An garzaya da dan wasan tawagar kwallon kafar Najeriya, Samuel Kalu zuwa asibiti, bayan da ya fati a lokacin atisayen tunkarar karawa da Burundi a gasar kofin Afirka.
Dan kwallon mai shekara 21, mai taka-leda a Bordeaux ya fadi ne a wajen atisaye a ranar Juma’a.
Najeriya za ta buga wasan farko a rukuni na biyu da Burundu wadda karon farko za ta fara buga wasannin a yanayin zafi da ake cewar zai kai 40C (104F) a filin wasa na Alexandria.
Hukumar kwallon kafar Afirka, Caf ta tsara cewar za a dinga yin dan takaitaccen hutu har karo biyu, domin bai wa ‘yan wasa damar shan ruwa kamar yadda dokar Fifa ta amince.
Kowanne wasa za a yi hutun minti uku a minti na 30 da fara tamaula da kuma minti na 70, domin bai wa ‘yan kwallo damar shan ruwa da kuma goge zufa.
Wannan ne karon farko da za ake buga wasannin cin kofin Afirka tsakanin Yuni da Yuli, inda aka yi hasashen cewar yanayi na zafi a Masar ya dan yi sama zai kuma ci gaba da zama a hakan zuwa watan gobe.