Dan wasan tsakiya Otavio ya bar Porto zuwa kulob din Al-Nassr na Saudiyya a kan yarjejeniyar kudi Yuro miliyan 60 wanda yayi dai dai da (dala miliyan 65.1), in ji kulob din Portugal a ranar Talata.
Otavio wanda haifaffen dan kasar Brazil ne ya koma Porto ne a shekara ta 2014 daga Internacional kuma ya fara buga wa kasarsa ta Portugal wasa a shekarar 2021, a cewar AFP.
KARANTA WANNAN: ‘Bada Hakuri Bai Wadatar Ba’ – Firaministan Sipaniya Ya Caccaki Rubiales Bisa Sumbatar ‘Yar Wasa Hermoso
Zai haɗu da abokin wasan Portugal Cristiano Ronaldo a Al-Nassr.
“Yana da wuya a bar kulob din bayan shekaru tara a nan,” dan wasan mai shekaru 28 ya shaida a gidan yanar gizon Porto.
Otavio ya zama sabon dan wasan da ya koma Saudi Pro League bayan manyan mutane kamar su Ronaldo, Karim Benzema, N’Golo Kante, Ruben Neves da Roberto Firmino da sauransu.
A wani labarin kuma,Da Dumi-Dumi: Henry Ya Sami Sabon Aikin Mai Horarwa
An baiwa tsohon dan wasan Faransa, Thierry Henry sabon nadin koci.
A cewar Fabrizio Romano, an nada Henry a matsayin sabon kocin tawagar Faransa U21.
Henry ya sanya hannu kan kwantiragi har zuwa shekarar 2025.
Kasar Faransa wadda ta lashe gasar cin kofin duniya za ta dauki nauyin ‘yan wasan da za su taka leda a gasar Olympics ta shekarar 2024 da Euro U21 a shekarar 2025.
Shahararren dan wasan Arsenal ya taba zama mataimakin kocin tawagar kasar Belgium.