Kusan ‘yan Ivory Coast 300 ne aka mayar da su gida daga Tunisiya, inda bakin haure suka ce ba su da kwanciyar hankali bayan da Shugaba Kais Saied ya ce suna haifar da barazana ga al’ummasa. Kamar yadda African News ta ruwaito.
Jakadan kasar Ivory Coast a Tunisiya, Ibrahim Sy Savane, ya ce an dawo da mutane 287 da suka hada da yara kanana 21 zuwa Abidjan a cikin wani jirgin sama mai saukar ungulu da aka yi hayarsa daga Habasha.
KU KARANTA: Yadda Gwamnatin Kano Ta Shiryawa Dokar Tsaftar Muhallin Karshen Wata A Gobe
Jakadan Ivory Coast a Tunisiya Ibrahim Sy Savane ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa, a baya-bayan nan, an dawo da jimillar ‘yan kasar Ivory Coast 1,053 daga Tunisiya tun lokacin da aka fara jigilar yan kasar a farkon Maris.
Shugaban kasar ta Tunisiya Kais Saied ya zargi , bakin haure 21 daga yankin kudu da hamadar Saharar Afirka da haddasa tashe tashen hankula da aikata laifuka, yana mai cewa suna da nufin “canza yanayin al’ummar Tunisiya da kuma raba ta da kasashen musulmi da ma na Larabawa.
Tunusiya, dake yankin arewacin Afirka mai yawan mutane miliyan 12, tana karbar baki kimanin 21,000 daga wasu sassan Afirka, wanda ke wakiltar kaso Sifiili da digo biyu na al’ummar kasar.
Sai dai a ‘yan kwanakin baya cikin jawabin Saied, ya ce bakin haure sun yi korafin an kai musu hare-haren wariyar launin fata kuma masu Dillalan gidaje sun kori da yawa daga cikin su a kan tituna saboda tsoron kar a ci su tara mai yawa ko kuma tura su gidan yari.
Kazalika Kusan ‘yan Ivory Coast 3,000 ne suka yi rajista da ofishin jakadancin kasar su don a mayar da su gida, a cewar Savane.
Yan Ivory Coast na iya shiga Tunisiya ba tare da biza ba, kuma kusan kimanin mutane 7,000 ke zaune a can, adadi mafi girma a yankin kudu da hamadar Sahara.
Yayin da wasu bakin haure na zuwa karatu, inda da dama na amfani da Tunusiya a matsayin matattarar ta yunkurin shiga Turai ta teku. Inda kuma Gwamnatocin kasashen Turai suka matsa wa Tunisiya lamba don ta shawo kan lamarin.
A wani labarin kuma, Dubu Ta Cika: EFCC ta Kama Malamin Addini Cikin Yan yahoo
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), a ranar Alhamis, 23 ga Maris din shekarar 2023, sun kama wasu mutane 28 da su ke zargin masu damfara ta yanar gizo ne a Ilorin, jihar Kwara. Kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
An kama wanda ake zargin ne a unguwar Mandate dake garin Ilorin, bayan bayanan sirri da hukumar ta ce ta samu kan ayyukan ‘yan damfara da ke yankin.