Babban hamshakin attajirin nan dan Afrika, Aliko Dangote, na kyautata zaton cewa sabon saka hannun jari na biliyoyin nairori a ɓangaren sukari zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da ba zai yi kasa da dubu 300 ba ga yan Nijeriya.
Sanarwar da Sashen Sadarwa na Kamfanin Aliko Dangote Group ya fitar ta rawaito Dangote ɗin na cewa kamfanin na samar da sabbin hanyoyin samun kudade don haka ya fadada ayyukansa a bangaren sukari.
KU KARANTA: Yar Takara Daya Tilo Ta Kaddamar da Yakin Neman Zaben Ta A Katsina
Dangote, wanda ke magana a wajen bikin bada lambar yabo ta shekarar 2022/2023 da aka yi a Numan, jihar Adamawa, ya ce damar da za ta samu za ta hada da ayyuka kai tsaye da kuma waɗanda ba na kai tsaye ba.
Dangote, wanda shi ne babban mai bayar da agaji a nahiyar Afirka, ya bayyana fatansa cewa dimbin jarin zai samar da ayyukan yi sama da 300,000 ga ƴan Nijeriya.
Ya ce, “Muna zuba jari mai yawa a jihar Adamawa ta hanyar fadada karfin tace sukari na DSR Numan daga 3000tcd zuwa 6000tcd, 9800tcd, zuwa 15,000tcd.
“DSR zai iya ƙirƙirar ayyuka kusan dubu ɗari uku, kai tsaye da kuma wanda ba na kai tsaye ba, tare da ingantattun tasirin ninkawa kan tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya,” in ji shi.
A shekarar 2010 ne aka zabi Dangote a matsayin shugaban kwamitin samar da ayyukan yi, a bangaren masu masana’antu.
A wani labarin kuma: FG Ta Tsawaita Ranar Fara Aikin Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna
Gwamnatin tarayya ta bakin ma’aikatar sufuri ta sanar da tsawaita wa’adin aikin layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.
Ministan Sufuri Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna ranar Lahadi a wani rangadin da ya kai don duba yanayin shirye-shiryen layin dogo na Abuja zuwa Kaduna kafin a fara aiki.