A ranar Litinin din da ta gabata ne dai darajar Naira ta fadi akan dala, inda aka yi musayarta kan N461.50 a kasuwar masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki, kamar yadda Nigerian Tribune ta rawaito.
Farashin ya nuna raguwar kashi 0.04 bisa dari idan aka kwatanta da N461.33 da aka yi musayarsa da dala kafin rufe kasuwancin a ranar 24 ga watan Maris.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Yankewa Wani Jami’in Zirga-Zirga Na Bogi Hukuncin Daurin Shekaru 2 A Gidan Yari
Budadden farashin ya rufe kan N461.75 zuwa dala a ranar Litinin.
Canjin N462.42 zuwa Dala shine mafi girman farashin da aka samu a ranar ciniki kafin ya kai N461.50.
Ana siyar da Naira a kan Naira 460 kan dala a kasuwar ranar.
An yi cinikin dala miliyan 101.77 a tagar masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki
A wani labarin kuma, An Kwaso ‘Yan Najeriya 151 Daga Kasar Libiya
Gwamnatin Tarayya da Hukumar Kula da ‘yan cirani ta Duniya (IOM) sun sake kwaso wasu ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Libya.
A cewar Ambasada Kabiru Musa, mai kula da ofishin jakadancin Najeriya a kasar Libya, wanda ya fitar da sanarwa a ranar Talata a Abuja, an dauko ‘yan kasar 151 daga Benghazi, yayin da gwamnati ke ci gaba da kwaso mutanen bisa son ran su.
Mutanen da aka kwaso sun hada da mata 71, maza 54, yara 14 da jarirai 13, sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a daren yau.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a shekarar 2022, IOM da Ma’aikatar Harkokin Waje, ta hanyar Ofishin Jakadanci a Libya, sun dawo da kusan ‘yan Najeriya 4,000.