By Abbas Yakubu Yaura
Ministan matasa da cigaban wasanni Sunday Dare ya nada tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Alhaji Abdullahi Abba Yola a matsayin shugaban ma’aikatansa.
Ciroman Yola wanda tsohon jigo ne a rusasshiyar hukumar wasanni ta kasa (NSC), ya kasance kai tsaye a harkar wasanni a matsayin dan wasa kuma mai gudanarwa tsawon shekaru da dama.
Wata sanarwa da ofishin ministan ya fitar a jiya ta bayyana cewa ana sa ran Abba Yola zai kawo kwarewarsa wajen gudanar da aikin da yake yi a yanzu.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ya samu kwarewar data dace a harkar gudanar da wasanni da za a iya amfani da ita don ingantawa da kyautata harkokin gudanar da kowace kungiya ta gwamnati, musamman a bangaren wasanni da matasa na kasar.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Abba Yola wanda ya yi wasanni a bangaren ayyuka daban-daban a kwanakin baya an saka sunan sa cikin mambobin kwamitin ministocin dake da alhakin samar da dawwamammen zaman lafiya a rikicin da ya dabaibaye hukumar kwallon kwando ta Najeriya NBBF.