By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan Najeriya shiyya 14 data kunshi jihohin Kaduna da Katsina, ta sanya ranar 23 ga watan Nuwamba zuwa ranar 6 ga watan Disamba domin tatance duba lafiyar ‘yan sandan da za a dauka aikin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Shehu Suleiman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar ranar Asabar a Katsina.
“za a gudanar da atisayen tantance lafiyar ‘yan sandan ne a yankin asibitin ‘yan sanda na Ibrahim Coomassie,dake Sabon-Layi, Katsina.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “An shirya gudanar da atisayen gwajin aikin duba lafiyar ne daga ranar Talata, 23 ga Nuwamba zuwa Litinin, 6 ga watan Disamba, 2021,” in ji shi.sannan kuma sanarwar taci gaba da cewa atisayen daukar ma’aikata kyauta ne kuma za a gudanar da shi bisa kyakkyawar al’ada ta gaskiya da kuma kwarewa.
Kazalika “An shawarci ‘yan takara da kada su bari ‘yan damfara ta yanar gizo da sauran masu aikata laifuka su yi amfani da tsarin daukar ma’aikatan wajen damfari wadanda ba su da laifi. Sannan “Ana gargadin dukkanku cewa duk wanda aka samu yana so zai karbi wani abu za a kama shi kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya” inji sanarwar.