Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce sake bude sansanin masu bautar kasa a Maiduguri da kewaye bayan shekaru 13, ba wai kawai ya nuna cewa an dawo da zaman lafiya da tsaro ba,kuma shaida ce da ke nuna cewa Borno gida ce da masu zuba jari.
A cewarsa, Allah Madaukakin Sarki da hazakar sojojin Nijeriya, yan sanda, DSS, da sauran jami’an tsaro tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force (CJTF).
Mafarauta da yan banga, sun taimaka wa Borno wajen tabbatar da tsaro. zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan rikicin Boko Haram na tsawon shekaru goma.
Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin bikin rantsar da kungiyar ‘B’ stream 1 Corps na shekarar 2023 da aka gudanar a sansanin horar da matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) na wucin gadi, Mustapha Umar El-Kanemi Arabic College, Maiduguri.
KARANTA NANTsaro Zai Bunkasa Nan Da Shekara Daya-Sabon Ministan Tsaro
Ya yi godiya ga Allah bisa wannan tafiya da aka yi wa daukacin yan kungiyar zuwa jihar, sannan ya bukaci wadanda ke son zuwa jihar da su yi la’akari da wannan aiki da suka yi a matsayin wani shiri na Allah.
Da yawa daga cikinku kun tuna cewa kusan shekaru 13 ba a gudanar da shirin na NYSC ba a jihar Borno, don haka ina yabawa ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da kungiyoyin tsaro da suka gabata kan dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Wannan kwas din Orientation mai dimbin tarihi ya kasance na musamman domin kawo karshen korar jami’an rundunar na Jihar Borno da aka kwashe tsawon shekaru ana yi wa wasu jahohi.
A WANI LABARIN KUMAKu Daina Bayyana Kasawar Yan Sanda A Soshiyal Media-IGP Ga Yan Nigeria
A nasa jawabin, kodinetan NYSC na jiha, Kwamared Mohammed Adamu Jiva, ya yi maraba da Gwamna Zulum da sauran baki da aka gayyata wajen bikin rantsarwar, ya kuma godewa gwamnan bisa samar da dukkan abubuwan da suka dace da suka sanya aka gudanar da kwas din Orientation.
Ya sanar da Gwamnan cewa an yi wa rijistar masu bautar kasa guda 1,125 wadanda suka hada da maza 629 da mata 496, inda ya kara da cewa daga cikin wannan adadi babu wanda ya kai rahoton wata matsala ta tsaro da ta shafi rayuwa da kuma dukiyoyi a tafiyar su zuwa jahar Borno.