A jiya Laraba Babban Lauyan gwamnatin Tarayya Kuma Ministan Shiri’a na Kasa Abubakar Malami ya ce nan bada jimawa ba, ofishinsa zai bi umarnin Kotu da ta bukaci a cire sashi na 84 sakin layi na 12, na sabuwar Dokar Zabe na shekarar 2022.
Wannan dai na zuwa ne a dai lokacin da Majalissar Dattijai dana Wakilai sukayi fatali da umarnin Kotun, inda kuma suka Sha-alwashin daukar matakin gaggawa kan lamarin.
Idan za’a iya tunawa dai, a ranar Juma’ar da ta gabata ne babban kotun tarayya dake zamanta a Umuahia ta bayyana sashi na 84 sakin layi na 12 a matsayin haramtacce, Wanda ya bukaci dukkannin Yan siyasa masu rike da mukaman nadi da su yi murabus kafin shiga zaben fidda gwani na jam’iyunsu.
Da yake zantawa da manema labarai Jim kadan bayan kammala taron majalissar zartaswa ta kasa a Abuja Malami ya ce, nan ba da jimawa ba, hukuncin Kotun zai fara aiki, domin kuwa tuni Shirye-Shiryen tabbatar da hakan yai nisa.
ULR