Sheikh Ahmad Gumi malamin addinin musulunci ne, likita ne wanda ya yi ritaya a matsayin kyaftin a rundunar sojojin Najeriya.
A cikin wata hira da aka yi a gidan Talabijin Siyasar Daily Trust, Malamin wanda ya taba ganawa daa ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma a lokacin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taka rawar sasanci tare da fitar da wasu da dama daga cikin Fulanin da ke dauke da makamai daga cikin daji kafin ya bar aikin.
Ya ce a shirye yake ya koma ya karasa abin da ya fara idan har akwai alkawari daga gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
KARANTA WANNAN Rundunar Soji Ta Bukaci Jami’anta Da Su Nesanci Harkar Siyasa
Ya kuma bayyana ra’ayinsa kan ritayar janar-janar na soja a duk lokacin da aka samu sabuwar gwamnati, yana mai cewa bai dace ba.
Menene ra’ayinka game da ritayar janar-janar sama da 100? Shin da gaske ne cewa bayan kowane sauyin sabuwar gwamnati ta yi ritayar manyan hafsoshin soja daga aiki Sojoji, na ruwa da na Sojan Sama?
Wannan abu ya fara ne a shekarar 1999 lokacin da aka siyasantar da wadannan mukamai. Sun rasa kwarewarsu. Jama’a na kallon irin alakarsu ta yanki, kabilanci ko addini, ba wai kawai kwararrun da ya kamata a ce suna irin wannan runduna ba.
Abin takaici ne matuka. Wani mummunan ci gaba ne da muka rasa jami’ai bayan horar da su, wasu daga cikin a kasashen waje.
Muna kashe makudan kudade wajen horar da su yaki iri-iri, sai kwatsam, saboda kabilanci, addini ko yanki, yawancinsu sun yi ritaya bayan nada wasu jami’ai.
Ka ga dai manyan jami’an soji ba sa barin karami ya shugabanci manyansa ko kuma a samu hutun sauya sheka, don haka sai a yi musu ritaya.
Kuma ba sai mun dora duk wanda yake karami saboda kabilarsa ko addininsa ko kuma daga inda ya fito ya shugabanci irin wannan runduna ba, musamman a wannan lokaci da babbar matsalarmu ta ita ce matsalar tsaro.
Muna buƙatar ƙwararrun hannaye, mutanen da suke da gogewa; mutane masu hankali kuma masu basira.
Ina fata yayin da muke haɓaka shirye-shiryenmu na siyasa za mu shawo kan wannan. Sojoji da bangaren shari’a su kaurace daga hannun ‘yan siyasa, in ba haka ba za a yi siyasar da zata lalata su. Ka ga sun mayar da rundunonin abin dariya.
A ma’aikacin gwamnati, dole ne wani ya yi shekaru 35 ko kuma ya kai shekaru 60 kafin ya yi ritaya; kana cewa an yi wa wadannan jami’an ritaya ne saboda siyasa? Shin wannan shine abin da ake samu a wasu ƙasashe?
Ayyukan tsaron mu na da matukar kulawa. Lokacin da Barack Obama ya zama shugaban kasar Amurka, ya bar dukkan shugabannin tsaro da jam’iyyar Republican ta nada saboda yaki a Iraki.
Ina ganin bai kamata mu taba sojoji da bangaren shari’a ba saboda kawai ana samun canjin shugabancin siyasa. Hatta ma’aikatan gwamnati yanzu abin ya shafe su.
Ya kamata a ce mukamin babban sakatare ya kasance na kwararrun ma’aikatan gwamnati ne kawai, amma sai ka ga yanzu ma an siyasantar da shi.
Siyasantar da kowane fanni na rayuwar al’umma na daga cikin fasadin da ke kara yaduwa a cikin al’umma.
A Wani Labarin Kuma Dawa Tai Nama: ‘Yan Sanda Sun Damke Mutane 207 Masu Sace Wayoyi Jama’a
‘Yan sanda sun kame wasu mutane 207 da suka yi awon gaba da wayoyin jama’a a jihar Kaduna cikin mako guda da ya gabata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige,ne ya bayyana hakan a Kaduna a ranar Asabar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.