- Hukumar tsaron farin kaya DSS tace da bankado wata kulla-kulla da wasu mutane ke shiryawa kan tsare gwamnan CBN Godwin Emefiele
- Hukumar ta bankado tsare-tsare da daidaikun mutane da kungiyoyi ke yi na cin mutuncin hukumar DSS da gwamnatin tarayya kan dakatar da binciken Emefiele
- Hukumar ta DSS ta yi kakkausa gargadi kan wadannan mutane dake yunkurin yin wannan kulle-kulle
Hukumar tsaron farin kaya DSS tace da bankado wata kulla-kulla da wasu mutane ke shirin yi kan tsare gwamnan CBN Godwin Emefiele.
Hukumar ta DSS ta ce gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele, ba a taba hana shi ganawa da lauyoyinsa da jami’an kiwon lafiya da kuma ‘yan uwansa ba,Punch ta rawaito.
Hakan na zuwa ne bayan wata babbar kotun birnin tarayya da ke zaman ta a Maitama ta umurci hukumar DSS da ta baiwa Emefiele damar ganawa da lauyoyinsa da iyalansa.
KARANTA WANNAN: An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Kara Yawan Kasafin Kudin Ilimi
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa an kama Emefiele ne a ranar 10 ga watan Yuni bayan da shugaban kasa, Bola Tinubu ya dakatar da shi, bisa dalilan yin garambawul a bangaren kudi da kuma gudanar da bincike a ofishinsa.
Sai dai wata sanarwa da kakakin hukumar, Peter Afunanya ya fitar ranar Asabar ta nuna cewa hukumar ta DSS ta bi ka’idojinta na gudanar da al’amarin Emefiele.
Sanarwar ta kara da cewa, “Yana da kyau a bayyana cewa hukumar ta baiwa iyalan Emefiele, likitocinsa da kuma wadanda suka dace damar zuwa ganin sa, tun daga ranar da aka kai shi ofishinta kafin kotu ta bukaci hakan.
“Ana aiwatar da ƙa’idodin Aiki akan Tsarin Gudanarwa kan waɗanda ake tuhuma da bincike ga na ƙarshe.
“Hukumar tana gudanar da harkokinta cikin gaskiya da sanin makamar aiki tare da mutunta doka tare da bin tsarin mulkin dimokradiyya.”
Afunanya ya kuma ce hukumar ta bankado tsare-tsare da daidaikun mutane da kungiyoyi ke yi na fara wani shiri na cin mutuncin hukumar DSS da gwamnatin tarayya kan dakatar da binciken Emefiele.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar DSS ta gano wasu mutane da kungiyoyin da ke shirin gudanar da zanga-zanga dauke da wasu kwaleya da alluna masu rubuce-rubuce don matsawa DSS da gwamnati ta dakatar da binciken Mista Godwin Emefiele.
“Irin wadannan kungiyoyi suna da niyyar haduwa a wurare daban-daban a Abuja da Legas nan da mako mai zuwa dauke da allunan da ke nuna alamun cin mutucin gwamnati tare da yin kira da a gaggauta sakin Emefiele.
Afunanya ya kara da cewa hukumar ta DSS tana kuma sane da shirin kutsawa cikin ma’aikatar domin yin amfani da ma’aikatan da ba su da aminci ga ‘yan ta’addan.
Afunanya ya gargadi wadanda ke yunkurin gudanar da wadannan ayyukan da su daina shirinsu nan da nan, ya kara da cewa, “Tuni ana sa ido kan su kuma za a kama su a lokacin da kuma idan ya zama dole.”
A wani labarin kuma, Ramaphosa Ya Buƙaci A Gaggauta Kawo Ƙarshen Yakin Ukraine
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da ke kasar Rasha a cikin tawagar masu neman zaman lafiya a ranar Asabar din da ta gabata ya shaidawa takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa ya zama dole a daina rikicin Ukraine.
A cewarsa Dole ne a sasanta wannan yakin ta hanyar tattaunawa da kuma hanyoyin diflomasiyya.