A Karon farko mutane sama da dubu hudu sun rasu sakamakon annobar Korona ta Covid-19.
Asibitoci a kasar sun cika sun batse yayin da majinyata da dama ke fama jiran yadda za a kula da su a wasu biranenn kasar, ind akuma yanayin harkar lafiya ke halin niyasu.
A yanzu haka kasar ta samu mutane sama da dubu dari uku da talatain da bakwai, adadin da ya sa kasar ta zamo ta biyu a duniya da cutar Korona ta hallakaq bayan Amurka dake matakin farko.
To sai dai duk da irin wannan mace-mace da ake samu, Shugaba Jair Bolsonaro na ci gaba da nuna adawar shi da dokar kulle da ake cewa na taiamakawa wajen dakile yaduwar cutar.
Ikirin shi na yin hakan shine dokar kulle ka iya illa fiye da ita kan ta cutar, inda kuma yace zai soke dokar da kotuna a kasar suka sanya.
A yanzu haka kasar Brazil na da mutane sama da miliyan sha uku da suka harbu da cutar kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar.