Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa gwamnan jihar Kano kan harkokin yada labarai, Abdullahi Umar Ganduje, wanda maigidan nasa ya kore shi har sau biyu, ya ce ba zai taba juyawa gwamnan baya ba duk da cewa jam’iyyun da suke daban-daban ne.
Daily Trust ta ruwaito cewa Ganduje ya kori Yakasai sau biyu saboda kalaman da ya yi kan yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da harkokin tsaro a kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN : Yan ta’adda Aka Saki, Aka Sako Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna– IPOB Ta Caccaki FG
Sai dai da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa bai taba furta kalaman batanci ga gwamnan ba duk da cewa dangantakarsu ta yi tsami, Yakasai ya ce yana da alaka ta uba da Ganduje baya ga shekaru shida da suka yi suna aiki tare.
Ya kara da cewa gwamnan bai sallame shi ba saboda ya na sukar gwamnatin jihar amma saboda kalaman da yake yi wa gwamnatin tarayya, yana mai cewa, an kore sane domin gamsar da manyan hukumomi.
Yakasai, wanda a yanzu ke neman ya gaji Ganduje a matsayin gwamna a karkashin jam’iyyar PRP, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a taron tattaunawa na 2023 da kungiyar ‘yan jarida ta jihar Kano ta shirya.
“Ba zan iya juyawa maigidana baya ba saboda wasu bambance-bambancen siyasa. Ban yi imani da irin wannan siyasa ba. Mun yi shekaru shida masu kyau kuma dole ne ya bar ni saboda maganganun da ba su dace ba da na yi ba wai gwamnatinsa ba amma ga gwamnatin tarayya,” inji shi.
Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu a shafin yanar gizo na Twitter, ya kuma karyata rade-radin da ake yi na cewa gwamnan ne ya dauki nauyin tsayawa takara a jam’iyyar PRP domin samun sauki ga dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, don samun nasara.
Da yake magana a kan shirinsa idan aka zabe shi a matsayin gwamna a 2023, dan takarar PRP ya ce za a tsara manufofinsa ne kan “kudurin 2033”, wanda zai mayar da Kano cibiyar bunkasar kasuwanci a yammacin Afirka.
Ya ce shirin na shekaru 10 zai mayar da hankali ne kan fannoni bakwai: bunkasar tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, muhalli, sake fasalin sassan gwamnati, da zaman lafiya da tsaro.
Ya kara da cewa sauke mulki ga jama’a daga tushe zai kasance kan gaba wajen cimma wannan tsarin.
A WANI LABARIN KUMA: Rasha Ta Kama Mutum 8 Da Take Zargi Da Kitsa Harin Gadar Crimea
Rasha tace ta kame mutum 8 da ke da hannu da harin ranar Assabar da aka kai wa gadar da ta haɗa Rasha da Criemea.
Hukumar tsaron kasar ta ce biyar daga cikin wadanda aka kaman yan ƙasar Rasha ne yayin da sauran yan kasar Ukraine ne da Armeniya