Dalibai a Nijeriya za su ci gaba da zama a gida duk da matakin da kungiyar ASUU ta dauka na janye yajin aikin da suka kwashe wata Tara suna yi. Matakin kin komawar daliban makaranta na zuwa ne bayan da aka fara bada hutun bukin kirsimeti da na sabuwar shekara.
Sannan har wala yau bayan karewar hutun kirsimeti da na sabuwar shekara, umurnin da Hukumar lura da jami’o’in Nijeriya ta bayar na rufe makarantun sakamakon dawowar cutar korona a karo na biyu.
A cikin mako guda kawai, an samu mutum 5, 000 da suke dauke da cutar korona a Nijeriya. Wanda shi ne adadin na farko da aka taba samu a Nijeriya tun bayan barkewar cutar.