Daga: Abbas Yakubu Yaura
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce duk wanda ya ce Najeriya na da kyau akwai bukatar a duba lafiyar sa, yana mai cewa bai kamata kasar ta kasance a inda take a halin yanzu ba.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata a wajen taron lacca na shekara 15 na gidauniyar Wilson Badejo a Legas, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: FIFA Za Ta Canza Ranar Fara Gasar Cin Kofin Duniya Na Kasar Qatar 2022
“Najeriya ba inda ya kamata ta kasance a yau. Idan wani ya ce babu laifi a inda muke a halin yanzu, to ana bukatar a duba kan mutumin ko yana da motsi,” in ji Obasanjo.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi zabin da ya dace a zabe mai zuwa domin a daidaita al’amura.
Ya kara da cewa, “Ko dai mu yi zabin da ya dace a 2023 domin idan muka yi zabin da ya dace za mu isa can.
“Duk da haka, idan ba mu yi zaɓin da ya dace ba a 2023, abubuwa za su cinye mu kuma mu yi addu’a a kan wannan. Dole ne mu yi zabi mai kyau a 2023.
“Abokina, marigayi Ahmed Joda, ya kasance yana gaya mani cewa Allah Ya ba mu duk abin da al’umma ke bukata kuma babu bukatar addu’a domin idan Allah Ya ba ka komai kuma ka yi almubazzaranci, to wani abu ya lalace.
“Na gaya masa cewa ko da a haka har yanzu muna bukatar addu’a a matsayinmu na al’umma domin abin da yake mai kyau yana bukatar addu’a sannan kuma a daya bangaren ma, muna bukatar karin addu’o’i.