ECOWAS vs Nijar: Dalilin da yasa Rasha za ta yi yunƙurin juyin mulki a Najeriya – Gargaɗi Ga Tinubu
Deji Adeyanju, wani mai sharhi kan harkokin siyasa, ya bukaci kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, da ta gaggauta daukar mataki kan Jamhuriyar Nijar.
Adeyanju ya yi gargadin cewa Rasha za ta iya yin yunkurin juyin mulki a Najeriya idan kungiyar ECOWAS ta gaza daukar kwararan matakai kan Jamhuriyar Nijar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Har Yanzu Ba’a Bamu Umarnin Shiga Nijar Ba-Sojojin Najeriya
Ya kalubalanci kasashen yammacin duniya da su kyale Afirka ta shawo kan kalubalen da take fuskanta.
Adeyanju ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: “Dole ne martanin ECOWAS game da juyin mulkin da aka yi a Nijar ya kasance cikin gaggawa da yanke hukunci; idan ba haka ba, Rasha za ta yi yunkurin juyin mulki a Najeriya nan ba da dadewa ba. Kamata ya yi a bar Afirka ta tafiyar da harkokinta da kanta.
“Ra’ayin samun sababbin shugabannin mulkin mallaka a cikin karni na 21 ba kawai abin ƙyama ba ne amma mai ban tsoro ne.”
Akwai rahotannin kungiyar ECOWAS na shirin mamaye jamhuriyar Nijar bayan hambarar da shugaba Bazoum da masu yunkurin juyin mulki suka yi.
A wani labarin kuma:Da Ɗumi:Ɗuminsa: NLC na gudanar da taron gaggawa kan dakatar da yajin aiki
Kungiyar kwadago ta Najeriya na cikin wani taron gaggawa na majalisar zartarwar ta kasa kan dakatar da yajin aikin da suka yi.
Wata majiya mai tushe a taron da ake ci gaba da yi a Abuja ta bayyana hakan ga jaridar DAILY POST a safiyar ranar Alhamis.