By Abbas Yakubu Yaura
Kimanin matasa 7000 da suka kammala karatun digiri da kuma matasa marasa aikin yi a jihar Edo suka ci gajiyar shirin horar da aikin yi wanda sanata Matthew Urhoghide yayi wanda aka fara tun daga shekarar 2016.
Mai taimaka wa Sanatan, kan harkokin yada kabarai Pet Eghobamien ne ya bayyana hakan, wanda ya kaddamar da horon kwana daya ga masu cin gajiyar shirin su 220 a Benin ranar Litinin, wanda Hukumar Cross River Basin ta dauki nauyinsa kuma Sanatan ya gudanar da shirin.
Eghobamien yace Sanatan na shirya horon ne akai-akai, inda ya kara da cewa, “A wannan horon na musamman, za a horar da mutane 200 kan kere-kere tare da asusun tashi da saukar jiragen sama na Naira 50,000, yayin da mutane 22 da za a horar dasu sana’ar gyaran gashi sannan za a ba su duk kayan aikin da ake buƙata don fara kasuwancin su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sanatan yace “Izuwa yau, mun horar da mutane 7,000. Ba ya iya horar dasu kawai mukeyi ba aa yana ƙarfafa musu giwwa, kuma ana yin horarwar akai-akai kuma akwai wani shirin horaswar wanda ke zuwa kafin lokacin Kirsimeti wanda zai ƙare kafin shekara ta ƙare.Za a ci gaba da horarwar a shekara mai zuwa Ya yi alkawari kuma zai cika.
“Wadanda suka ci gajiyar a baya suma sun sami abin da suke bukata don fara kasuwancin su. Ga masu sana’ar wanzanci, mun basu komai, gami da samar da saitin da za su fara. Abin da kawai suke bukata shi ne su sami shago su fara sana’ar.”