Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta kama wasu mutane 5 da ake zargi da yin amfani da takardun jabu na ofisoshin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da babban lauyan gwamnatin tarayya da kuma ministan shari’a wajen karbar kudi daga hannun wasu jama’a da ba su ji ba basu gani ba.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN: Najeriya Na Gargarar Mutuwa Karkashin Mulkin Tinubu, Inji PDP
Wadanda ake zargin sun hada da Bashir Ladan, Yakubu Hamza Mohammed, Mohammed Bello, Adamu Ibrahim, da Steven Anom.
A cewar sanarwar, wadanda ake zargin sun hada baki ne tare da yin amfani da takardun bogi wajen samar da aikin yi na bogi da wasikun shawarwari kan kudi ga jama’ar da ba su ji ba basu gani ba.
Sanarwar ta kara da cewa, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala cikakken bincike.
A wani labarin kuma, Yadda Jami’an Kwastam Suka Ki Karbar Cin Hancin N50m A Hannun Wani Da Ake Zargi
Jami’an da ke Tincan Island na Hukumar Kwastam ta Kasa ta ce ta ki amincewa da cin hancin Naira miliyan 50 da wani da ake zargin dan fasa kwauri ne da ke shigo da kwayoyin Tramadol da sauran magunguna ya bayar domin sakin kwantenar kayansa.
Kwanturolan hukumar kwastam na yankin Tincan, Mista Adekunle Oloyede, ya bayyana hakan a ranar Litinin din nan yayin da yake jawabi ga manema labarai a shedikwatar rundunar.
Ya ce wanda ake zargin, Mista Boniface Ike, ya amince da mallakar kwantena biyu masu kafa 40 da aka kama dauke da kwayoyi wadanda kudinsu ya kai Naira miliyan 550.
Ya kara da cewa kudin da wanda ake zargin ya kawo za a bayar da shi ne a matsayin na goro.