Hukumar hana cin hanci da rashawa ta Najeriya ta gayyaci tsohuwar ministar jin dadi da takaita aukuwar ibtila’I ta kasar Hajiya Sadiya Umar Farouk kan zargin ta da karkatar da sama da naira biliyan 37, ko kuma aka karkatar da su a karkashin ikonta.
Hukumar ta bukaci ministar ta amsa gayyatar a shalkwatar ta da ke babban birnin kasar Abuja ranar laraba mai zuwa don yin cikakken bayani game da yadda wadannan kudi suka bata ko sama ko kasa.
Karanta nanJam’iyar APC Ta Bukaci A Aje Bangaranci A Hada Hannu Don Ciyar Da Nijeriya Gaba
Sadiya Faruk na cikin ministocin Buhari da aka rika zargin su da cin hanci tun suna kan karagar mulki, duk da dai ta sha musanta zarge-zargen da ake yi mata.
EFCC din ta zargi Sadiya da hada kai da wani mutum mai suna James Okwete wajen wawure wadannan kudi, sai dai tuni Sadiyar ta ce ko sunan mutumin bata taba ji ba.
Bayanai na nuna cewa James ya shafe kusan kwanaki 10 a hannun jami’an na EFCC, inda suke gudanar da bincike.
Daga tsohuwar ministar har masu bata shawara da mataimakanta kan harkokin yada labarai sun ki yiwa manema labarai karin haske kan wannan lamarin.
A wani labarin kumaJami’an Tsaro Sun Kubutar Da Mutane 21 Da Akayi Garkuwa Dasu A Jahar Kogi
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya bayyana matukar damuwarsa game da gagarumar wahala, tashe-tashen hankula, da masifu masu alaka da yanayi da aka fuskanta a duniya baki daya a cikin shekarar 2023.
A cikin sakonsa na sabuwar shekara kafin zuwan 2024, Guterres ya bayyana shekarar 2023 a matsayin shekarar da ta fi zafi a tarihi, yana mai cewa, “Dan Adam na cikin zafi. Duniyarmu tana cikin hadari. Ana samun murkushe mutane ta hanyar karuwar talauci da yunwa. Yaƙe-yaƙe suna ƙaruwa da yawa da tashin hankali. Kuma amana ta yi karanci.