EFCC ta Gurfanar da Shugaban Kamfanin Mai bisa zargin Damfarar Banki Biliyoyin Kuɗaɗe
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da Shugaban kamfanin man fetur a gaban kuliya bisa zargin damfarar banki Naira Biliyan 4.4.
A ranar Alhamis ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da Shugabar Kamfanin Emee Oil And Gas Nig Ltd Florence Onojame a gaban kuliya bisa zargin damfarar Bankin Access har Naira Biliyan 4.4.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta samu labarin cewa Misis Onojame ta bayyana a gaban wata kotun laifuka ta musamman da ke Ikeja tare da kamfaninta bisa tuhumar ta da laifin haɗa baki da kuma karɓar Biliyoyin Kuɗaɗe daga Banki ta hanyar zamba.
Sai dai wadda ake tuhumar ta ki amsa laifin da ake tuhumar ta, yayin da Lauyan EFCC, Fatai Mohammed, daga nan ya miƙa buƙatar sa ga kotun da ta ɗage zaman Shari’ar tare da ci gaba da tsare wadda ake tuhuma.
KARANTA NAN:Yajin Aikin NLC: Shettima ya Jagoranci Taro da masu ruwa da tsaki a Aso Rock
Mohammed ya shaida wa kotun cewa wadda ake tuhumar ta aikata laifin tare da wasu mutane huɗu a wani lokaci a watan Fabrairun 2022 a Jihar Legas.
Lauyan ya ce wadda ake zargin ta saci Naira biliyan 4.4 ta zamba ta hanyar Primus Plus wani dandali na banki na Bankin Access ta hanyar amfani da bayanan shiga kamfanin ta.
Ya ƙara da cewa, wanda ake ƙara ya ƙara tura kuɗaɗen zuwa wasu asusu da dama da ke cikin bankin.
Lauyan mai gabatar da ƙara ya ƙara da cewa wadda ake tuhumar ta rike hannun jarin Naira Miliyan 100 a asusunta na Bankin Access da sunan kamfaninta sannan kuma ta tura kuɗaɗen zuwa asusun ajiya na Total Energy Nig Ltd da sanin hakan laifi ne.
Sai dai lauyan mai kare wanda ake tuhuma, Williams Onate ya sanar da kotun cewa an gabatar da bukatar belin wanda yake karewa a gaban kotu inda zai gabatar da shi gaban kotu yayin zama na gaba.
Za mu bukaci da a ɗage zaman zuwa ɗan takaitaccen lokaci da kuma duba buƙatar bayar da belin wadda ake tuhuma da ya ci gaba da kasancewa a hannun EFCC,” in ji Onate.
A cewar EFCC laifukan da ake zargin sun ci karo da sashe na 278,326 da 409 na dokar laifuka ta Jihar Legas da akayi ma kwaskwarima a shekarar 2015.
Mai shari’a Mojisola Dada ta bayar da Umarnin a ci gaba da tsare wadda ake ƙara a gidan yari na Ikoyi har sai an saurari buƙatar belin ta.
Dada ya dage ci gaba da sauraron ƙarar har sai ranar 10 ga watan Oktoba domin sauraron buƙatar belin.