Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da wani mutum mai matsakaicin shekaru, Obakin Emmanuel Ajibola, a gaban kotu bisa zargin satar Naira miliyan 251.6 a Ibadan.
Sai dai wanda ake zargin ya ki amsa tuhumar da ake masa na tuhume-tuhume hudu.
KARANTA WANNAN: KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Shettima Zai Wakilci Shugaba Tinubu a Wani Muhimmin Taro a Cuba
Obakin wanda ya gurfana a gaban babbar kotun jihar Oyo, ana zarginsa da damfarar wani kamfani mai suna Lee Gakino Nigetia Limited kudi har naira miliyan dari biyu da hamsin da daya da naira dubu dari shida da tamanin da biyar.
An gurfanar da shi ne a kan tuhume-tuhume 4 da suka shafi sata. An ce an aikata laifin ne a ranar 20 ga watan Disambar shekarar 2022, a Ibadan.
Sai dai wanda ake zargin ya ki amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake tuhumar sa da aikatawa, inda mai shari’a Ladiran Akintola na babbar kotun jihar Oyo ya bayar da belinsa kan kudi Naira miliyan 50.
A cewar sanarwar da EFCC ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban yada labaranta, Wilson Uwujaren, wanda ake tuhuma yana daya daga cikin daraktoci biyu na kamfanin Lee Fakino Nigeria Limited kuma mai sanya hannun a asusun kamfanin.
Ana zarginsa da fitar da wadannan makudan kudade daga kamfanin Lee Fakino Nigeria Limited ba tare da izinin Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Akindele Fajemiyo, wanda kuma shi ne mai sa hannun a asusun kamfanin.
Har ila yau, ana zargin wanda ake tuhuma da cire lambobin waya da adiresoshin imel na MD kuma shugaban kamfanin daga bayanan bankin Lee Fakino Nigeria Limited, ta hanyar da ake samun sanarwar hada-hadar kasuwanci ta cire kudi, don ba shi damar ci gaba da bin diddigin lamarin asusun.
Bayan haka, wanda ake tuhuma ya janye wannan adadin daga asusun kamfanin, wanda kudin ne da aka biya na ayyukan da Lee Fakino Nigeria Limited ya aiwatar na ma’aikatar noma ta jihar Legas tsakanin ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2022, da 9 ga watan Maris, 2023, ba tare da wata sanarwa da Fajemiyo ya damu ba.
Da aka gurfanar da shi a gaban kuliya, ya amsa cewa “ba shi da laifi” a kan tuhumar da EFCC ta yi masa.
Da yake amsa rokonsa, lauyan masu shigar da kara, Oyelakin Oyediran, ya bukaci kotun da ta dage zaman shari’a tare da roko ga kotun da ta tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali har sai an yanke hukunci.
Lauyan wanda ake kara, Ibrahim Lawal, ya bukaci kotun da ta shigar da wanda yake karewa domin a bayar da belinsa.
Mai shari’a Ladiran Akintola ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira miliyan 50 da kuma mutum biyu wadanda za su tsaya masa, musamman matarsa da kanin wanda ake kara, a irin wannan adadi.
Bugu da kari, “wadanda za su tsaya musu za su yi rantsuwar kama aiki, su ajiye katin shedar su na zama ‘yan kasa a gaban kotu, sannan su samar wa kotu isassun adiresoshin zama”.
Har ila yau, kotun ta umurci wanda ake kara da ya baiwa kotun katin shedarsa na zama dan Kasa da adireshinsa na zama.
An dage sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Oktoba, 2023, don ci gaba da sauraren karar.
A wani labarin kuma, NIS Ta Kawar da Fasfo 60,000 A Cikin Kwanaki Hudu – Minista
Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo, yace an kawar da fasfo 60,000 a cikin kwanaki hudu na aiki.
Mai baiwa ministan shawara kan harkokin yada labarai, Babatunde Alao, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne da safiyar yau yayin da yake karbar bakuncin ministar agaji da yaki da fatara, Beta Edu.