Hukumar EFCC ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da mai shari’a Charles Agbaza na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke ranar Juma’a, wanda ya yi watsi da karar da ake yi wa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Mista Babachir Lawal.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Da yake yanke hukunci kan karar da aka shigar kan Babachr Lawal da sauran wadanda ake tuhumar, mai shari’a Agbaza, ya ce hukumar EFCC da ta gabatar da shaidu 11 a shari’ar ta kasa gabatar da hujjojin zargin aikata laifin.
Ya ci gaba da cewa, EFCC ba ta tabbatar da cewa Lawal mamba ne a kungiyar Presidential Initiative for North East da ta bayar da kwangilar ba.
KU KARANTA KUMA Kotu Ta Wanke Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Daga Zargin Almundahana
Ya kara da cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ba ta kuma tabbatar da cewa Lawal mamba ne a kwamitin kula da kwangilar ministocin da ya tantance tare da bada amincewar kwangilar ba.
Kakakin hukumar ta EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya bayyana a ranar Juma’a a Abuja, duk da haka, za ta samu kwafin hukuncin don ta yi nazari cikin gaggawa tare da kalubalantar ingancinsa a kotun daukaka kara.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Lawal da kanin sa Hamidu Lawal da Suleiman Abubakar da Apeh Monday tare da wasu kamfanoni biyu Rholavision Engineering da Josmon Technologies.
Ana tuhumar su ne da laifin almundahana, da karkatar da naira miliyan 544 na ciyawar da aka sare. (NAN)/Solacebace
A Wani Labarin Kuma Dalilin da ya sa ban maida hankali na a kafofin Sadarwa ba — Tinubu
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Ahmed Tinubu, ya bayar da dalilan da ya sa ya daina maida hankali kan kasidu da labarai da kuma batutuwan da suke taso wa a shafukan sada zumunta.
Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana cewa idan da yana karanta labarai a shafukan sada zumunta da ya kamu da ‘ hawan jini’.