El-Rufa’i Ya Raka Uba Sani Birnin Gwari Don Tattaunawa Da Masu Ruwa Da Tsaki
Gwamnan Jahar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya raka Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Uba Sani wajen wani tattaunawa da masu ruwa da tsaki na Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar.
Ɗan Takarar Gwamnan Sanata Uba Sani ya bayyana haka a shafin sa na Facebook, inda ya bayyana cewa ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Kaduna wajen neman goyon baya da tattaunawa da masu ruwa da tsaki na yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin APC Na Rivers: Tinubu Amaechi ya zaɓa – Eze ya mayarwa Okocha martani
A cewar sa, a lokacin sun samu tattaunawa mai matuƙar mahimmanci da masu ruwa da tsaki, da Mata da Ƙungiyoyin Matasa na yankin.
A lokacin ziyarar, sun kuma kai ziyarar Bangirma Ga Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubair Mai Gwari II wanda ya yi masu Kyakkyawar tarba, tare da yi masu addu’a.
Ya rubuta a shafin sa na Facebook kamar haka “Tare da Mai Girma Gwamna Mal. Nasir El-Rufa’i, mun kai ziyara zuwa karamar hukumar Birnin Gwari inda muka tattauna da masu ruwa da tsaki da kungiyoyin mata da matasa.
A garin Birnin Gwari mun kai ziyarar Bangirma ga mahaifinmu Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubair Jibril Mai Gwari ll wanda ya sanya mana albarka da addu’a.