Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce bullo da biyan kudaden da ma’aikatar ilimi ke yi ta hannun shugabannin makarantu bai dace da manufofin gwamnati ba, don haka bai kamata ba.
A cewarsa, ya kamata a soke shi ba tare da bata lokaci ba, sannan a mayar da duk wasu kudade da aka karba nan take.
KARANTA KUMA El-rufa’i Na Daf Da Rufe Makarantun Kiyon Lafiya A Kaduna
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Wani taro na musamman na majalisar zartaswar jihar Kaduna da aka gudanar a ranar Litinin 7 ga watan Nuwambar 2022, ya bayyana samar da ilimi kyauta na tsawon shekaru 12 na karatu a matsayin wani ci gaba na gwamnatin jihar.
Jaridar Daily Trust ta tuna cewa a kwanan baya ma’aikatar ilimi ta bukaci dalibai su biya kudin makaranta a fadin jihar.
Wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Mista Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu a ranar Talata ta bayyana cewa, taron na musamman na majalisar zartarwa ta jihar Kaduna ya tattauna kan takardar da ma’aikatar ilimi ta bayar kan samar da kudade mai dorewa don kula da kayayyakin makarantu.
Mai ba da shawara na musamman ya ci gaba da cewa, “Majalisar zartarwa ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta ci gaba da aiwatar da tsarin karatun sakandare kyauta tare da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na makarantun gwamnati.
A Wani Labarin Kuma Duk Da Aikin Bankin Duniya, Al’ummomi A Bauchi Sun Rasa Ruwan Sha
A halin yanzu al’ummomi da dama a jihar Bauchi irinsu Wunti Dada, Gudum Hausawa, Gudum Sayawa, Rafin Makaranta, Turum, da Inkil sun rasa ruwan sha, duk da cewa sun ci gajiyar aikin samar da ruwan sha na Naira biliyan 20 da bankin duniya ya dauki nauyi.
Aikin ruwan an yi shi ne da nufin inganta samar da ruwan sha a cikin babban birnin Bauchi da wasu kauyukan da ke makwabtaka da su.