Rahotanni sun bayyana cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi wa mataimakin gwamnan babban bankin Kasa CBN mai kula da manufofin tattalin arziki Kingsley Obiora tambayoyi.
Binciken da jaridar Daily trust ta gudanar a ranar Asabar din nan ya nuna cewa, tambayoyin wani bangare ne na zarge-zargen almundahanar kudi a karkashin Gwamna Godwin Emefiele da ke tsare a hannun ‘yan sandan sirrin kasar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaitp cewa Wata majiya a CBN ta yi zargin cewa kwamitin bincike na musamman da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kafa domin gudanar da bincike kan zaman Emefiele na iya taimakawa wajen gayyatarsa a wani mataki na ganin ya tsaya a matsayin shaida.
KARANTA WANNAN DSS Sun Sake Samun Wata Nasarar Kan Hadimar Emefiele A Kotu
An tattaro cewa Obiora, wanda ke tare da tawagar masu binciken tun ranar Laraba, ya tabbatar da cewa an sake shi.
Hakazalika binciken mu ya nuna cewa kwamiti na musamman karkashin jagorancin Jim Obazee yana yiwa mataimakan gwamnonin babban bankin CBN tambayoyi, da sauran manyan jami’an bankin, a wani bangare na binciken da ake yi.
DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Majiyar ta ce, “Bari mu fito fili mu bayyana. Babu wanda ke zargin Dr Obiora da zamba ko sata. Dr Obiora, kamar sauran mataimakan gwamnoni, kwamitin ya yi masa tambayoyi da yawa kafin a sako shi.”
A Wani Labarin Kuma Kotu Ta Daure Mutum Takwas Bisa Aikata Laifin Zamba A Sokoto, Da Abuja
Akalla mutane takwas ne aka yankewa hukunci tare da dauresu bisa laifin zamba a Sokoto da Abuja.
Mai Shari’a M.U. Dogondaji na babbar kotun jihar Sokoto ya yanke wa biyu daga cikin wadanda ake zargin, Sanni Dikko da Naabu Umar hukunci, bisa laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma aikata zamba cikn aminci.
Dikko dai ya hada baki da Umar wajen karbar kudi naira 1, 500,000 daga hannun wanda ya kai kara mai suna Mustapha Mudashir a wani cinikin fili.
“Bincike ya nuna cewa Dikko, a baya ya sayar da fili ga wani Ashiru Muhammed, ya sa Umar ya gabatar da kansa a matsayin wanda ya mallaki filin domin ya shawo kan Mudashir ya sayi kadarar kan kudi Naira miliyan 1.5.
“Mudashir yana cikin aikin ginin filin ne a lokaci sai ainihin mai filin ya dakatar da shi.