Yanzu haka dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sallami Graham Potter daga matsayin kocinta, Daily Post ta rawaito.
Kungiyar ta Premier ta tabbatar da hakan a wata sanarwa data fitar a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Leicester City Ta Sallami Kocinta Brendan Rodgers
Mai haɗin gwiwa na Blues ne ya nada Potter a watan Satumba don maye gurbin Thomas Tuchel.
Sai dai kuma an kore shi da wata bakwai a kwantiragin shekaru biyar da ya rattabawa hannu.
Potter ya lashe wasanni bakwai ne kacal a cikin wasanni 22 da ya yi a gasar Premier.
Ficewar tasa ta biyo bayan rashin nasarar da Chelsea ta yi a gidan Aston Villa da ci 2-0, wanda hakan ya sa Blues ta zama ta 11 a teburin gasar Premier, inda yanzu aka samu tazarar maki 12 tsakaninta da Manchester United da ke matsayi na hudu.
A wani labarin kuma, Abba Gida Gida Ya Ci Gaba da Shirin Karban Mulki, Ya Kara Wani Muhimmin Naɗi
Zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Abdullahi Ibrahim Rogo a matsayin shugaban tsare tsare na lokacin mika mulki.
Wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin mika mulki na gwamnan jihar Kano 2023 na jam’iyyar NNPP Dr. Abdullahi Baffa Bichi ta nuna cewa nadin zai fara aiki nan take har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Zababben Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce nadin nasa ya samo asali ne a bisa tarihi da jajircewarsa da kuma biyayyarsa daga 2019 zuwa 2023.