FAAC Ya raba N907bn Ga Jihohi
Kwamitin rabon asusun tarayya ya ce ya raba N907.05bn a tsakanin matakai uku na gwamnati a watan Yunin 2023.
Adadin ya nuna cewa an samu raguwar N120.89bn idan aka kwatanta da N786.16bn da aka raba a watan Mayun 2023, kuma shi ne mafi girma a wannan shekarar kuma karo na biyu bayan koma bayan da aka samu tun watan Janairu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Farashin Man Fetur: Dalilan Da Suka Sanya Ma’aikatan Zamfara Ke Zuwa Wurin Aiki Sau Biyu
FAAC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a karshen taronta na baya-bayan nan a Abuja ranar Alhamis.
Sabon Akanta Janar na Tarayya, Dr Oluwatoyin Madein ne ya jagoranci taron.
Hukumar ta PUNCH ta lura cewa karuwar da aka samu a watan Mayu ya haura na watan Yuni duk da cire tallafin man fetur.
Sanarwar ta kara da cewa, “Jimillar kudaden shigar da ake rabawa N907.05bn sun hada da kudaden shiga na doka na N301.50bn, kudaden harajin da za a raba na N273.23bn, kudaden da aka samu na harajj na yanar gizo na N11.44bn da N320.89bn.”
Gwamnatin Tarayya ta samu N345.56bn, Jihohin kuma sun samu N295.95bn, Kananan Hukumomi sun samu N218.06bn, yayin da Jihohin da suke hako mai suka samu N47.48bn (kashi 13 cikin 100 na kudaden shiga na ma’adinai).
An kuma bayyana cewa an samu babban kudaden shiga na N1.15tn na watan Yunin 2023, wanda ya haura N701.79bn da aka samu a watan da ya gabata da N451.13bn.
Sanarwar ta kara da cewa, “Daga kudaden shiga na N301.50bn da aka raba bisa ka’ida, gwamnatin tarayya ta samu N146.71bn, gwamnatocin Jihohi kuma sun samu N74.41bn, Kananan Hukumomi sun samu N57.37bn. An raba Naira biliyan 23.01 ga jihohin da abin ya shafa a matsayin kashi 13 cikin 100 na kudaden shiga.
A wani labarin kuma:Tinubu ya fara wani yunkuri na kawo cikas ga Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa – Zargin Atiku
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Face Of Waziri-Nigeria (FOWN) ta yi zargin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na yin kokari wajen ganin ya hana akalla biyu daga cikin alkalan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa yin murabus, ta yadda za su yi wa kwamitin shari’a cikas.
Darakta Janar na kungiyar, Kwamared Bukky Adeniyi, ya yi wannan zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli, 2023.
Adeniyi ya bayyana cewa, idan aka yi la’akari da tanadin doka da ake da shi, wanda ya sa a sauya da kuma dawo da shi idan wani alkali ya yi murabus daga mukaminsa, wata dabara ce ta hana dokar shari’a aiki da kuma tasiri.