A cigaba da kai ziyarar ta’aziyya ga Iyayen yarinyar nan mai shekaru 5 a Kano Hanifa Abubakar, mai dakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta kai ziyarar ta’aziyya ga Iyayen ta.
Dimokuradiyya ta bada rahoton a makon da ya gabata ne aka sami gawar yarinya Hanifa bayan wanda ake zargi Malaminta ne ya sace ta tare da kasheta kuma ya bunneta a makarantar.
Da ta ke bayyana alhini kan lamarin Hafsat Abdullahi Ganduje ta nuna matukar alhininta game da danyan aikin da Malaminta ya aikata.
Daga bisani ta sha alwashin tsayawa tsagin da ka wajen ganin an kwatowa yarinyar hakkinta.
Mai dakin gwamnan ta sami rakiyar Shugaban karamar hukumar Nasarawa Honarabul Auwalu Shu’aibu Aranposu, da shugabar Mara ta jam’iyyar APC Hajiya Fatima Abdullahi Dala, da Ma’ajin Jam’iyyar Hajiya Yardada MaiKano Bichi, da sauran masu baiwa gwamna shawara kan fannonin daban-daban na jihar Kano.