Farfesa Maƙari Ya Yi Jinjina Ga El-Rufa’i Da Uba Sani Kan Namijin Kokarin Su
Shehun Malami Kuma babban limamin masallacin Najeriya dake Abuja Sheikh Ibrahim Ahmad Makari ya jinjinawa El-Rufa’i kan ayyukan cigaba da ya shimfida a Abuja da Kaduna, da kuma bayyana fatan cewa Uba Sani zai ɗora daga inda ya tsaya.
A wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani an hango shi yana cewa “Malam Nasir El rufa’i ya cancanci jinjina, na da’de ina neman irin wannan damar a inda zan fadi inda ba zai zama kamar tumasanci ba, indai ana maganar jagorancin ne to babu kamar El-Rufa’i.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Duminsa: INEC Ta Dakatar Da Zaben Sanata A Wata Jiha
A cewar sa wani daga cikin ministoci da suka ya shaida mashi cewa dukkanin ministocin da suka biyo baya haryanzu abinda ya yi bai kai abinda yayi shi ka’dai a babban birnin tarayya ba.
Ya ƙara dacewa “Gaskiya Muna jinjina Masa da irin Ayyukan da yayi a wannan Jaha ta mu ta birnin tarayya Abuja.
Ya bayyana cewa Sanata Uba sani zai iya abinda El-Rufa’i ya yi na Alkhairi, sai ya yi addu’a da Allah ya Kara daukaka ya Kara taimako yasa adace.
Sheikh Ibrahim Ahmad Makari mutum ne mai taka tsan-tsan ga lamarin siyasa an sheda yana kokarin kamanta gaskiya