- Rundunar shiyar Ilorin ta hukumar EFCC a ranar Laraba, ta gurfanar da wani fasto Temidayo Eseyin, bisa zarginsa da damfarar jami’ar Landmark, Omu-Aran tsabar kudi Naira miliyan 19.3.
- An gurfanar da Faston ne biyo bayan wasu tuhume-tuhume hudu da suka hada da karkatar da kudaden jami’ar a gaban mai shari’a Funsho Lawal
- Faston wanda ya kasance lauya ga Jami’ar Landmark, ya samu damar mallakar kadarorinta, takardun mallakarta da kuma kudade
Rundunar shiyar Ilorin ta hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, a ranar Laraba, ta gurfanar da wani fasto mazaunin Ilorin na cocin Living Faith da aka fi sani da Winners Chapel, Temidayo Eseyin, bisa zarginsa da damfarar jami’ar Landmark, Omu-Aran, jihar Kwara. Naira miliyan 19.3, Punch ta tawaito.
Eseyin, lauya ne kuma tsohon mamba a kwamitin ladabtarwa na kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Ilorin, an gurfanar da shi ne a kan wasu tuhume-tuhume guda hudu da suka hada da karkatar da kudaden jami’ar a gaban mai shari’a Funsho Lawal na babbar kotun jihar Kwara da ke zaune a Ilorin.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Tinubu Zata Ba da Fifiko Kan Bangaren Kiwon Lafiya — Fadar Shugaban Kasa
A cikin wata takardar koke ga EFCC, Eseyin, yayin da ya ke lauya ga Jami’ar Landmark, ya samu damar mallakar kadarorinta, takardun mallakarta da kuma kudade.
A matsayin da aka dauka, an yi zargin cewa Eseyin yana “zamba, cin hanci da rashawa.
Musamman a daya daga cikin laifukan da ake zarginsa da aikatawa, wanda ake tuhumar, tsakanin shekarar 2014 zuwa 2022, ya mallaki wata kadara da aka fi sani da “Old Midland Building” na jami’ar Landmark, dake kan titin Emir/Obbo Road, Ilorin, mai haya Eseyin da ya karba na tsawon shekaru 8, kuma bai iya samar da wurin ba.
Mai shigar da karar ya kuma yi zargin cewa Eseyin ya yi yunkurin sayar da kadarorin ne ba tare da umarnin jami’ar ba, don haka ya mika koke ga EFCC.
A wani labarin kuma, Wani Dan Majalisa Ya Tona Asirin Abinda Ya Haddasa Rikicin Manoma Da Makiyaya
An gano cewa neman cikakken iko da rabon albarkatun kasa a matsayin babban musabbabin tashe tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma a jihar Taraba.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Takum I a majalisar dokokin jihar, Abubakar Tonko, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai a karamar hukumar Wukari.