By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta tabbatar da mutuwar mutane 31 a wani turmutsutsun da ya afku a wani taron coci a Fatakwal, babban birnin jihar a ranar Asabar.
Rundunar ta kuma bayyana cewa wadanda suka samu raunuka “an yi gaggawar kwashe su zuwa asibiti domin jinya cikin gaggawa”.
2023: Kwankwaso Ya Musanta Karbar Dala $660,000 Daga Hannun Wike Na Wakilan PDP Na Kano
A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Grace Iringe Koko, ta ce binciken farko da rundunar ta gudanar ya nuna cewa “abin takaicin ya faru ne a lokacin da mahukuntan Majami’ar suka shirya wani yakin neman zabe wanda ya jawo hankulan jama’a”.
An yi nufin da cewa cocin zata ba da kayan abinci ne ga marasa galihu.
‘Yan sandan sun ce taron ya kasance “ba za a iya shawo kan sa ba” kuma “duk kokarin da masu shirya taron suka yi na ganin sun shawo kan lamarin yaci tura”.
Kwamishinan ‘yan sanda, Friday Eboka, yayin da yake Allah wadai da lamarin, ya umarci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sashen binciken manyan laifuka na jihar da ya gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin.
Ya kuma yi kira ga kungiyoyin addini da na agaji da su tabbatar sun hada kai da ’yan sanda wajen samar da tsaro da kula da jama’a wajen shirye-shiryensu a nan gaba.
Kwamishinan ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka mutu tare da yin addu’ar Allah ya jikan su ya kuma basu ikon jure wannan rashi.
Comments 1