Ma’aikatar Tallace-tallacen Waje DOAS, Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA), ta ce gwamnatin ta yi asarar kusan Naira miliyan 500 na kudaden shiga a gidajen hasumiyar turakan sadarwa da aka gina ba tare da izini ba.
Daraktan sashen, Dakta Babagana Adam, ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Da Wasu Jagorori 48 Za Su Halarci Taron Shugabannin Amurka Da Afirka
Ya ce akwai bayanan da aka samu tare da FCTA tun lokacin da aka kafa sashen sun nuna cewa matsugunin hasumiyar turakan sadarwa 3,050 da aka gina a cikin birni ba su da sahihancin amincewa.
Daraktan ya ce wasu kamfanoni sun biya ne kawai don ba da izini, sun ki biyan kudin sarrafa su na Naira miliyan 1.5m, sannan suka ci gaba da kafa turakan sadarwa da hasumiya, wanda ya bayyana a matsayin haramtaccen tsari.
Adam ya ce: “Mun yi asarar kusan Naira Miliyan 500m a matsayin kudaden shiga daga baraguzan gine-gine na hasumiya a yankin.
“Izinin kafa katafaren gini Naira 20,000 ne, kudin sarrafa shi ne Naira miliyan 1.5, amma da yawa ba sa biya, takardar izini kawai suke biya kuma su ci gaba da gina matsuguni da hasumiyar sadarwar.
“Mun gano hakan ne a lokacin da wasu al’ummomi suka gabatar da kokensu ga Majalisar Dokokin kasar cewa hayaniyar da ta tashi daga hasumiya ta shafe su, don haka akwai bukatar a magance su.
Ya bayyana cewa hasumiyar sadarwa 320 ne kawai aka tabbatar dasu a Abuja. Ya kara da cewa galibin masu amfani da wayar salula suna nema ne kawai ba tare da biyan kudaden da ake bukata ba.
A wani labarin kuma, Irin abinda ya faru a Chattam House shine zaku yi tsammani idan Tinubu yaci zaɓe a 2023 — APC
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana ganawar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu ya yi a gidan Chatham House da ke birnin Landan a matsayin wani kyakkyawan zato na abin da ‘yan Najeriya za su yi tsammani daga shugabancinsa a shekarar 2023.
Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma, Muhammad Molash a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce hakika wannan dama ce ga Tinubu ya nuna kwarewarsa ta jagoranci ga al’ummar duniya, da hangen nesan sa ga Najeriya, da tarihinsa na kishi da kuma iya kokarinsa wajen gano masu hazaka da kuma wakilta nauyin da ke kansu.
Jam’iyyar ta dage cewa fitar da gwanin ya kuma nuna cewa shi ne dan takarar shugaban kasa mafi shiryawa a Najeriya.