Duk da korafe-korafen yawaitar jami’o’i a Najeriya, taron majalisar zartarwa ta tarayya da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta ya amince da ba da lasisi ga sabbin jami’o’i 37 a kasar nan.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa ta ranar Litinin,kamar yadda Daily Post ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Wata ‘Yar Najeriya Ta Karya Tarihin Gasar Dafa Abinci Ta Duniya
Ya ce ci gaban ya kawo adadin jami’o’in da gwamnatin Buhari ta bawa lasisi zuwa 72 tun daga shekarar 2015.
Sai dai kuma ya kasa bayyana sunayen jami’o’in, amma ya bayyana cewa daya daga cikinsu jami’a ce ta yanar gizo, wacce ita ce irinta ta farko a Najeriya, kuma mallakar wata mata ce daga jihar Bauchi, tare da sa ran za ta dauki nauyin irin wadannan matan musulmin Arewa ko an hana su halartar zuwa harabar jami’oin .
Da yake gabatar da tambayoyi kan fa’idar karin jami’o’in idan aka yi la’akari da kalubalen samar da kudade na wadanda ake da su, Adamu ya bayyana cewa wadannan duk na sirri ne, suna da isassun kudaden tafiyar da su, kuma bai kamata a hana su damar wanzuwa ba.
Ministan ya ci gaba da bayanin cewa a zahiri Najeriya na bukatar karin jami’o’i saboda wadanda ake da su ba su isa su dauki dukkan masu sha’awar neman ilimi ba.
A wani labarin kuma, Badakalar Kudade: Kotu Ta Dage Shari’ar Da Akewa Mompha, Ta Sanya Sabuwar Rana
Mai shari’a Mojisola Dada ta kotun laifuffuka ta musamman da ke zamanta a Ikeja, Legas, a ranar Litinin, 15 ga watan Mayu, 2023, ta dage ci gaba da sauraren karar da ake zargin Ismaila Mustapha, wanda aka fi sani da Mompha da laifin damfarar Naira Biliyan N6bn kan rashin zuwan lauyansa.
Mai magana da yawun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da wakilinmu ya samu a daren ranar Litinin.