…Majalisar zartaswa ta tarayya FEC ta amince da wasu kwangiloli don samar da wasu kayayyaki na zamani da za a yi amfani da su a aikin kidayar jama’a.
Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) a ranar Laraba ta amince da wasu kwangiloli biyu na Naira biliyan 15.3 don samar da kayan aikin shigar da kayayyakin fasahar sadarwa da na’urorin taimaka wa kidayar jama’a a shekarar 2023.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ne ya bayyana haka bayan taron majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa, da ke Abuja, ranar Laraba.
KU KARANTA KUMA Buhari na Jagorantar FEC Tun Bayan Kammala Zabukan 2023
Shehu ya ce: “Daga cikin bayanan da aka amince a yau akwai bayar da kwangilar samar da kayan fasahar sadarwa da kere-keren kayan sadarwa (ICT) don kidayar jama’a a shekarar 2023.
“Wannan don hukumar kidaya ta kasa (NPC). Ana nufin ƙidayar jama’a. An bayar da kwangilar bangaren ICT akan kimanin Naira biliyan 10.9.
“Wata kwangilar da aka amince da ita ga hukumar kidaya ta kasa ita ce kwangilar haɓakawa da aiwatar da hanyoyin sarrafa na’urorin wayar hannu don taimakawa na’urorin zamani da za a yi amfani da su don ƙidayar jama’a a shekarar 2023.
“Wannan ya kai kimanin Naira biliyan 4.4.”
Shehu ya ce majalisar ta kuma amince da kwangilar ci gaban kudin ababen more rayuwa a waje a sabuwar makarantar horas da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC kan Naira biliyan 3.3.
Ya kara da cewa an amince da Naira biliyan 1 daidai wa daida don kwangilar siyan motoci 19 ga hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA).
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Mai taimaka wa shugaban kasar ya ce majalisar ta amince da Naira miliyan 65 don bambanta kudin da ake kashewa wajen samar da kayan kashe gobara a filayen jiragen sama a ma’aikatar sufurin jiragen sama.
A Wani Labarin Kuma NPC Ta Sanar Da Ranar Fara Kidayar Jama’ar Najeriya
Hukumar kidayar jama’a ta kasa ta bayar da bayanai na karin haske kan kidayar jama’a ta shekarar 2023.
Hukumar ta ce an shirya dukkan tsare-tsare don fara lissafin gini da jerin sunayen gidaje nan da ranar 17 ga Afrilu, kafin a fara aikin kidayar jama’a a watan Mayu. Daily Post ta ruwaito.