Gwamnatin tarayya ta amince da fara hutun haihuwa na kwanaki 14 ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa hutun an amince da bayar da shi ne, ga mazan da matansu suka haihu.
KU KARANTA: Gwamnan Arewa Ya Amince a Zaftarewa Ma’aikatan Jiharsa Albashi
To sai dai sanarwar ta ce mazan ma ba kowa ba, sai wanda matan su suka yi haihuwa ta farko zuwa ta huɗu.
Dokta Folasade Yemi Esan, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya (HoCSF), a ranar Litinin, a cikin wani sako mai taken ‘Kididdigar hutu bisa kwanakin aiki da amincewa da izinin haihuwa a ma’aikatun gwamnati.
Ta bayyana cewa ya yi daidai da tsarin aikin gwamnati da Dokokin Ma’aikata 2021 ya samar.
Idan za ku iya tunawa a watan Satumba ne Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC) ta amince da hutun haihuwa ga mazajen da za su kulla alaka mai kyau da jaririn da suka haifa ko kuma su karbe shi.
A wani labarin kuma: Jihohi 3 ne kawai ke samar da kuɗin shiga fiye da abinda ake turo masu – Dr Ayawei
Shugaban Hukumar Tattara Harajin na Jihar Bayelsa, Dokta Nimibofa Ayawei, a jiya ya ce jihohin Legas, Ogun, da Kaduna ne kadai ke samun kudaden shiga na cikin gida, wanda aka fi sani da Internal Generated Revenue, IGR, sama da kason da ake samu daga Hukumar Bayar da Kudi ta Tarayya, FAAC.
Dokta Ayawei wanda ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da Cibiyar Harajin Haraji ta Najeriya karo na 47, CITN, ya bayyana cewa sauran jihohin sun dogara ne kawai ga FAAC wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na ‘yan kasa, yana mai jaddada bukatar jihohi su kara himma wajen bunkasa IGR.