A wani yanayi na kaka-nika-yi, gwamnatin tarayya ta fara biyan malaman jami’o’in da ke sassan kula da nazarin kiwon lafiya a wasu jami’o’in gwamnatin tarayya bashin albashin da suke bin ta.
Malaman dai suna karkashin kungiyar kwararrun likitoci ta Najeriya, daya daga cikin kungiyoyin biyu da gwamnati ta baiwa lasisin rage tasirin kungiyar malaman jami’o’i.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Dage Sauraren Karar da Obi Ya Shigar Akan Tinubu
A shekarar 2022 ne gwamnati ta aiwatar da dokar ba aiki ba albashi ga malaman jami’o’i na tsawon watanni bakwai sakamakon yajin aikin da kungiyar ASUU ta shiga.
Yunkurin ganin gwamnati ta biya malaman albashin da aka hana su na tsawon yajin aikin da ASUU ta yi ya ci tura.
Sai dai kungiyar Likitocin a Najeriya, kungiyar da ta kunshi likitocin da ke cikin malamai da sauran likitoci, ta bayyana wa gwamnati cewa ba a rufe makarantun likitanci a lokacin yajin aikin ba, don haka bai kamata a rika ƙin biyan albashin mambobinsu ba.
Da yake zantawa da wakilinmu a Abuja, wata majiya daga Jami’ar Nnamdi Azikiwe ta tabbatar da cewa an biya malaman aikin likitancin albashin da aka hana su.
A wani labarin kuma: Zan Tabbatar Alaƙa Ta Ɗore Tsakanin Amurka Da Najeriya ~ Tinubu
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi alkawarin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen hada kan kasar nan, bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Ya kuma tabbatar da cewa a shirye yake, domin ci gaba da tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin Najeriya da kasar Amurka.