Gwamnatin tarayya ta fara rabon kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a yankin Neja Delta a shekarar 2022. Kamar yadda The Nation ya ruwaito.
Ma’aikatar kula da yankin Neja Delta a ranar Litinin ta mika kason kudin tallafin na jihar Rivers ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) domin rabawa duk wadanda abin ya shafa a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Shari’ar PDP Da Tinubu
An kaddamar da rabon tallafin ne da aka yi wa lakabin na farko na taimakon jin kai ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a yankin a shekarar 2022 a dakin ajiyar NEMA da ke Fatakwal a ranar Litinin.
Kayayyakin da za a raba sune buhunan kayan abinci, tan na kayan gini, da dai sauransu.
Da yake jawabi a wajen bikin, Ministan hula da harkokin Neja Delta, Umana Okon, ya nuna nadamar yadda cewa yankin ya fi fuskantar bala’i sakamakon yanayin da ake ciki.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: El-Rufai ya tsige wasu sarakunan Gargajiya A Kaduna, ya kori wasu hakimai
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya amince da tsige sarakunan Piriga da Arak, Mai Martaba Jonathan Paragua Zamuna da Mai Martaba Janar Aliyu Iliyah Yammah (mai ritaya). Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Kwamishiniyar kananan hukumomin jihar, Hajiya Umma Ahmad ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce, an sallami sarakunan biyu daga mukamin su a ranar Litinin 22 ga watan Mayun 2023.