Shugabancin PDP ya shiga tsilla-tsilla a yayin da jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta yi yunkurin zawarcin gwamnonin jihohin Zamfara, Bello Matawalle da na Bauchi Bala Mohammed da na kuma Kuros Ribas Ben Ayade domin ganin sun dawo Jam’iyyar ta APC.
Tattaunawar zawarcin wanda gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni zai jagoranta, wanda dama shi ne shugaban jam’iyyar APC din da kuma gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Wata majiya mai karfi a APC ta shaidawa majiyarmu cewa; Gwamna Ifeanyi Uguwanyi na jihar Inugu ma APC din na son zawarcinsa, sai dai shi bai nuna sha’awarsa na shiga APC din ba.
APC sun ce babban burinsu shi ne su samu akalla gwamnoni uku daga kudu maso gabashin Nijeriya cikin biyar da ake da shi kafin zaben 2023. “idan ba mu samu Ifeanyi Uguwanyi ba, zamu tabbatar da mun lashe zaben jihar Anambra wanda za a gudanar nan bada jimawa ba”, ya tabbatar.
Bayanai sun nuna cewa; manyan jiga-jigan APC a Zamfara, kamar su Ahmed Yerima, sun amince Gwamna Matawalle na jihar ya dawo jam’iyyar, inda Yerima ma ya fito ya bayyana cewa Matawalle zai fice a PDP.