Kimanin yara miliyan 10.4 a kasashe bakwai, ciki har da Najeriya, za ta yi fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a shekarar 2021, in ji masu tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
“Yayin da 2021 ke gabatowa, UNICEF ta damu matuka game da lafiya da jin daɗin yara miliyan 10.4 da aka yi hasashen za su yi fama da mummunan yunwa a shekara mai zuwa a waɗannan ƙasashen,” in ji sanarwar, inda ta ambaci ƙasashen da abin ya shafa a matsayin Jamhuriyar Congo (DRC), Najeriya, Burkina Faso, Mali, Niger, Sudan, Sudan ta Kudu da Yemen.
UNICEF ta ce rashin tsaro a DRC, sakamakon zamantakewar tattalin arziki na cutar coronavirus da takaitaccen damar samun muhimman ayyuka zai haifar da kimanin yara miliyan 3.3, kasa da biyar, wanda zasu yi fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a shekara mai zuwa. A arewa maso gabashin Najeriya, sama da yara 800,000 ake sa ran za su yi fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki, ciki har da kusan 300,000 wadanda aka kiyasta suna fuskantar barazanar mutuwa, a cewar UNICEF, mafi yawan yara tun daga 2013.
Kimanin miliyan daya da dubu dari hudu, za su fuskanci matsanancin rashin abinci mai gina jiki a Sudan ta Kudu a shekara mai zuwa, saboda rikice-rikicen da ke faruwa, rashin tsaro, da kuma karancin kula da lafiya, ruwan sha da tsafta. A Burkina Faso, Mali da Niger, adadin yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki na iya ƙaruwa da kaso 21 cikin ɗari zuwa miliyon biyu da digo tara a cikin rikice-rikice, kaura da muhalli a waɗannan ƙasashe na Tsakiyar Sahel.
UNICEF ta kuma yi gargadin cewa yara sama da miliyan 2 da ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a Yaman kuma ana sa ran adadin zai karu a shekarar 2021. Tun farko UNICEF ta nemi karin dala biliyan 1 daga masu ba da tallafi don tallafawa shirye-shiryen samar da abinci mai gina jiki ga yara a kasashen da ke cikin matsala a 2021. ya kuma bukaci masu ba da agaji da masu ba da tallafi na kasa da kasa da su fadada hanyoyin samun tallafi ga ayyukan agaji