By Abbas Yakubu Yaura
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya, CP Frank Mba, ya mika ayyukan sashen hulda da jama’a na rundunar ga mataimakinsa, CSP Olumuyiwa Adejobi.
Adejobi ya karbi ragamar kula da sashen nan take, in ji SP Benjamin Hundeyin na sashin hulda da jama’a a hedikwatar rundunar a ranar Asabar.
Sanarwar mai taken, ‘CP Frank Mba ya mika wa mataimakin sa yayin da yake kan hanyarsa ta NIPSS’.
A wani bangare an karanta cewa, “Wannan canjin ya biyo bayan nadin CP Mba wanda babban sufeto-Janar na ‘yan sanda ya yi na ai kashi babban kwas a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Kasa, Kuru dake Jos.
“Olumuyiwa Adejobi, babban Sufeton ‘yan sanda, tsohon dalibi ne a babbar jami’ar Ibadan inda ya karanta ilimin kimiyya da kayan tarihi, da kuma Ilimin nazarin kasa (a hade da girmamawa). Ya kuma yi Digiri na biyu a fannin Zaman Lafiya da Rikici daga Jami’a guda.
Sannan ya “taba zama jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) a rundunar ‘yan sandan jihar Ogun daga shekarar 2008 – 2016; sannan ya zama PPRO a Hedikwatar shiyya ta 2, Onikan dake Legas, a shekarar 2016 baya da haka ya zama PPRO a Rundunar ‘yan sandan jihar Legas tsakanin watan Satumbar shekarar 2020 zuwa Agusta 2021. CSP Olumuyiwa kwararren mai sadarwa ne kuma manajan hoto wanda ya samu nasarori sosai a mukaman da ya rike a baya.”
Comments 1