Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta gargadi jam’iyyu da ‘yan siyasa da su guji wuce gona da iri da kuma tukin ganganci ya yin yakin neman zabe.
Shugaban rundunar, Dauda Biu a ranar Talata, ya shaida wa direbobin ayarin motocin da su rika kula da ababen hawa cikin taka tsantsan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NiMet Ta Yi Hasashen Samun Saukar Ruwan Sama Da Wuri a 2023
Gargadin na Biu ya biyo bayan hadurran motoci da yawa da wasu suka yi sanadiyar rasa rayuka, da ya shafi mambobin jam’iyyar da magoya bayanta.
A wata sanarwa da jami’in kula da ilimin jama’a na rundunar Bisi Kazeem ya fitar, ya bukaci direbobin da su bi ka’idojin zirga-zirga domin gujewa afkuwar hatsari.
Shugaban rundunar ya ce duk da gargadin da hukumar ta FRSC ta yi, da yawan masu ababen hawa na karya dokokin da aka kafa.
Kazeem ya ce “An umurci jami’an kwamandan da su inganta ganin kungiyoyin sintiri a wurare masu mahimmanci,” in ji Kazeem.
Biu ya kuma yabawa jam’iyyu da ’yan takara da suka bi ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa.
Hukumar ta sanar da tura karin motoci masu aiki da ma’aikata don yakar irin wadannan munanan dabi’u.
A wani labarin kuma, Buhari Ya Nada Tsohon IGP A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Ayyukan ‘Yan Sanda
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da nadin tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, Solomon Arase (mai ritaya) a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda.
Shugaban a wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, ya ce nadin ya zo daidai da tanadin sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.