Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya ta ce ta kwato motoci sama da 385 da aka sace tun bayan kaddamar da shirin tantance ababen hawa na kasa.
Jami’in kula da ilimin jama’a, Bisi Kazeem, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa daya fitar ranar Litinin a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: JAMB Ta Sanya Ranar Fitar da Sakamakon Jarabawar UTME 2023
A cewarsa, hukumar ta FRSC ta samu gagarumar nasara tare da bullo da shirin NVIS a fannin tattara bayanan sirri da musayar bayanai.
Ya ce hakan ya taimaka wajen kwato motocin da aka sace tare da samar da “hukumomin tsaro da isassun bayanan sirri don hanzarta bin diddigin masu aikata laifuka.”
“Saboda haka, yana da matukar muhimmanci a sanar da jama’a cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata kadai, hukumar FRSC ta kwato motoci sama da 385 da aka sace a Najeriya.
“Wannan ya faru ne ta hanyar kayan aikin NVIS da sauran dabarun aiki,” in ji Kazeem.
Ya ce daga cikin motocin da aka kwato kwanan nan akwai wata motar tirela da aka sata a cikin kwantena mai lamba BEN 477 XC.
Kazeem ya ce motar ta lalace ne a mahadar jami’ar Babcock da ke Ilishan, kuma sai da hukumar FRSC ta janje motar daga kan hanya domin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa.
“Daga baya an gano ta ta hanyar bincike mai zurfi cewa motar sata ce,” in ji shi.NAN
A wani labarin kuma, UTME 2023: JAMB Ta Sauya Ranar ‘Yan Takarar da Basu Sami Damar Rubuta Jarabawa ba
Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, ta ce za ta sake sanya sunayen ‘yan takarar da basu sami damar rubuta jarabawar UTME ba.
Hukumar, a cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar ranar Litinin, ta sanar da cewa duk wadanda basu sami damar zana jarabawar UTME na shekarar 2023 a cikin lokacin da aka kayyade ba tare da wani laifin nasu ba, za a sake zana jarabawar zuwa ranar Asabar, 6 ga watan Mayu, 2023.