FRSC Zata haɗa hannu da Jahar Akwa Ibom domin sanya alamu, ƙa’idojin tuƙi akan hanya
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa tace a shirye take domin haɗa hannu da Gwamnatin Jahar Akwa Ibom domin tabbatar da cewa hanyoyin ta an gyara su da alamu da ake amfani dasu akan hanyoyi.
Kwamandan Kwalejin Ma’aikata dake Enugu Assit. Corp Marshall Chidiebere Benjamin Ukwota, wanda ya Jagoranci Dalibai ya zuwa ziyara ga Gwamna Udom Emmanuel, ya bayyana haka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani ya zaɓi Mataimakiyar El-Rufa’i, Hadiza Balarabe a matsayin abokiyar takarar sa
A cikin wata sanarwa daga Ekikere, Sakataren Ƴan Jarida na Mataimakin Gwamnan, Moses Ekpo ya bayyana haka a ranar Litinin, yace Ukwota ya yabawa Gwamnatin Jihar da irin namijin ƙoƙarin ta wajen samar da nagartattun hanyoyi da suka haɗa Al’ummomi.
Ya bayyana yunkurin sanya alamomin a matsayin wata dabara da ake amfani dashi a hanyar Nijeriya, da suka shafi samar da kyawawan hanyoyi.
Ya bayyana cewa Ɗaliban sun zo ziyarar ne a Jahar ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da samun gogewa.
“Abinda suke nazari akan shi, an yi mashi take da “maida hanyoyin Nijeriya zuwa Mataimaki na Duniya”.
Da yake maida jawabi, Emmanuel wand ya samu wakilcin Mataimakin sa Moses Ekpo ya nuna Jindaɗinsa na yabawar da Hukumar FRSC tayi na samar da nagartattun hanyoyi a Jahar.
“Idan muna da kyawawan hanyoyi, saboda mun bada fifiko wajen haɗa al’ummatai, domin zai taimaka wajen fito da kayayyakin amfanin gona daga wani wuri zuwa wani wuri.
“Samun hanyoyi masu alamu da ƙa’adoji zai taimaka wajen rage Haɗurra, kuma Gwamnati tana da sha’awar haɗa hannu domin tabbatar da tsaftar hanyoyi,” Inji Gwamnan.
Ya ƙara dacewa Gwamnatin Jahar a shirye take domin haɗa Al’ummatai ta hanyar kyawawan hanyoyi.