Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin bayar da sabon gida da tsabar kudi Naira miliyan 3 ga wata ‘yar asalin jihar, Aisha Abubakar Dorayi, wadda ta zama ta biyu a gasar Karatun Al-Qur’ani ta duniya ta shekarar 2022, wadda aka gudanar a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Dubai,Daily Trust ta rawaito.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi wannan alkawarin ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jiha a gidan gwamnati dake Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Tasa Keyar Jami’in Bogi Na Wata Hukuma Gidan Yari
Ya ce shawarar da aka yanke na baiwa wanda ta yi nasara kyautar shi ne don karfafa wa sauran ‘yan asalin jihar kwarin gwiwa don ganin sun yi fice.
“Wannan nasara ba ga Aisha kadai ba, ba ga iyayenta kadai ba, a’a ga jihar Kano ne. Don haka ne muka yanke shawarar zaburar da ita da kyautar gida a cikin gidajen malamai na jihar. Mun kuma yanke shawarar bayar da tsabar kudi Naira miliyan uku ga yarinyar. Muna alfahari da ita,” in ji Ganduje.
Da take jawabi bayan sanarwar, wacce ta lashe kyautar, Aisha Abubakar Dorayi daga karamar hukumar Gwale ta jihar ta yaba da wannan karimcin tare da yin alkawarin dorewar wannan aiki.
Ta godewa iyayenta da malamanta da abokan aikinta da suka karfafa mata gwiwa don samun ilimi har zuwa irin wannan matakin.
“Na yi matukar farin ciki a yau da gwamnatin jihar ta amince min da wannan nasarar. Amma nasara tamu ce, musamman malamaina da iyayena. Sun tsaya tare da ni don cimma wannan a yau. Ba zan iya gode musu ba. Allah ya saka musu da alkahair duka,” ta yi godiya.
A wani labarin kuma, Kwamitin Gudanarwar APC Ya Gaza Cimma Matsaya Kan Shugabancin Majalisa Ta 10
Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar All Progressives Congress APC na kasa ya gaza yanke shawara kan batun yankin da zai shugabanci majalisar dattawa da na majalisar wakilai ta 10 a taron da ya yi a Abuja ranar Laraba.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa hukumar NWC ba za ta iya daukar matsaya kan tsarin shiyya-shiyya ba sai da shawarar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya je Fatakwal domin kaddamar da wasu ayyuka da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya aiwatar a lokacin taron.