By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kano ta umarci hukumar samar da ruwan sha mai tsafta RUWASSA da ta gaggauta gyara rijiyoyin burtsatse da suka lalace a kananan hukumomi takwas na cikin manyan biranen jihar domin dakile matsalar karancin ruwan da ake fama da ita.
DUBA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: Sojoji Sun Harbe Kwamandan Kungiyar IPOB A Jihar Imo
Umurnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun Mista Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Abdullahi Ganduje.
Mista Anwar ya ce Gwamna Ganduje, wanda mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf-Gawuna ya wakilta, ya ba da umarnin a wani taro da jami’an ma’aikatar albarkatun ruwa; RUWASSA da shugabannin kananan hukumomi takwas.
Anwar ya ruwaito Gwamna Ganduje yana cewa: “Ya kamata kuma RUWASSA ta dauki nauyin kididdiga na musamman a kananan hukumomi 44 da ke bukatar rijiyoyin burtsatse, tare da la’akari da wasu abubuwan da ke tattare da yawaitar rijiyoyin burtsatse ga muhalli.”
Gwamnan ya kuma umurci kananan hukumomin cikin manyan biranen jihar da su yi amfani da tankuna motoci wajen raba ruwa ga mazauna garin a matsayin mafita cikin gaggawa.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta karfafa hadin gwiwa da Hukumar FDA domin samar da mafita na tsawon lokaci domin inganta samar da ruwan sha a jihar. (NAN)
Comments 1